✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai kararrakin zaben fidda gwani 600 a gaban kotu —INEC

Akwai wata jam’iyya ita kadai ta shigar da korafi 70 a makon jiya.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce yanzu haka akwai korafe-korafe 600 a gaban kotu daban-daban da ke kalubalantar zabukan fidda gwanin jam’iyyu.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a yayin taron bita ga Alkalai kan al’amuran da suka shafi Babban Zabe na 2023.

Yakubu ya kuma ce INEC din ta yi nazarin hukunce-hukuncen kotunan daban-daban da aka yi tun daga zabukan fidda gwani, zuwa na gwamnoni, hadi da na cike gurbi da aka gudanar zuwa yanzu.

“Mun gano wuraren da ya kamata mu kawo gyara don rage yawan shigar da kara, kuma sakamakon haka, muka samu raguwar kararrakin da ke kalubalantar zaben da muka aiwatar.

“Sai dai fa kararrakin zabukan da jam’iyyu suka gudanar na karuwa sosai, domin ko makonni biyu da suka gabata, sai da wata jam’iyya ita kadai ta shigar da korafi 70, tana neman mu amince da nada ko sauya ‘yan takararta, duk da cikar wa’adin yin hakan a jadawalin Zaben 2023.

“Wannan matsalar na kawo cikas ga shirye-shiryen gudanar da Babban Zaben da su kansu kotunan da dole za su ci gaba da wasu shari’un har bayan zaben.”