✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai fa’ida a kasuwancin kayan marmari – Alhaji Tijjani

Alhaji Tijjani Abdullahi mai sana’ar sayar da kayan marmari ne a gefen rukunin Gidajen Alhaji Sani Zangon Daura da ke unguwar Kado da ke Abuja.…

Alhaji Tijjani Abdullahi mai sana’ar sayar da kayan marmari ne a gefen rukunin Gidajen Alhaji Sani Zangon Daura da ke unguwar Kado da ke Abuja. Ya tattauna da Aminiya dangane da sana’arsa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Yaushe ka fara wannan sana’a?
Na samu shekara 15 ina yin wannan sana’a inda na fara garin Nyanya da ke kusa da Abuja. Amma a nan kasuwar kayan marmari a unguwar Kado da ke Abuja na shekara takwas ina baje koli da zaman lafiya da kowa da kowa da ni da ma’aikata da sauran abokan zama baki daya.
Duka kayan nan, a nan muke gyara su idan an debo  su daga gona sai mu wanke don a saye su da tsafta wato ciki lafiya, baka lafiya.
Aminiya: Ya kuke da mahukuntan gwamnati iri-irin na Abuja?
Suna hana wadanda suka karya doka ne, amma mu muna kokarin kiyaye wa. Domin muna kwashe bola mu dura su a buhu mu adana har a zo a kwashe ba ma son shara. Don ba a son datti da karya doka a Abuja. Duk kuma wanda aka kama shi to ya sha wuya matuka. Akwai fa’ida a kasuwancin kayan marmari.
Aminiya: Me kuke sayarwa?
Wannan kasuwa ta kayan marmari muna sayar da kayar marmari da kayan lambu ko da rani ko da damina. Muna sayar da namu da aka saba da su da ma wadanda ba a saba da su ba, wato irin na Turawa da na kasashen China. Wasu kuma ana kawo mana irin ne kamar irin albasan kasar China wacce muke yafawa mu yi ban ruwanta har ta girma mu debo mu gyara mu sayar. Muna ce mata Chai domin albasa ce wacce ba ta da jan-kwallo irin na mu sai dai kawai ta na da lawashi.
Sauran ba su da suna a harshen Hausa kamar su koriyanda, Falak da Larabci ko falalan-Alayahho, da fasli irin na Kano da na Jos, hendibe, ba’ale, ganyen kori, mint, rashad, fis, da dai sauransu.
Aminiya: Idan mutum ya zo neman abu babu ya kuke yi?
Idan muna da wurin da za mu samo, sai mu karbi lambar waya, idan an samo mu kira mutum mu sanar da shi.
Aminiya: Kuna yin kwangila zuwa otel ko manyan gidajen abinci?
Gaskiya ba ma yi, sai dai mutum ya zo ya saya, domin muna gudun wahalar biyan kudi da sauransu.
Aminiya: Ya kuke yi lokacin damina?
Muna da shirin kare kannu, amma yawancin kayan ai ba ruwanshi da rowan sama.
Aminiya: Kun kai mutane nawa a wannan wuri?
Muna da yawa, za mu kai kimanin 20 domin kowa da bangarensa.