✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Akwai dimbin arziki a harkokin kasuwanci’

An shawarci matasan kasar nan da su rika shiga cikin harkokin kasuwanci, ta yadda za su kasance masu dogaro da kansu tare da  rage dogaro…

An shawarci matasan kasar nan da su rika shiga cikin harkokin kasuwanci, ta yadda za su kasance masu dogaro da kansu tare da  rage dogaro da samun aikin gwamnati musamman a wannan hali da duniya ke ciki na matsin tattalin arziki.
Wani matashin dan kasuwa da ke Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Rabi’u Dungurawa shi ne ya yi wannan tsokacin a wata zantawa da ya yi da Aminiya, ya ce yana da kyau matasan kasarnan su zamo masu dogaro da kansu ta yadda za su ci gaba da ba da tasu gudummawar ga ci gaban tattalin arziki da kuma zamantakewa. Saboda akwai dimbin arziki a harkokin kasuwanci.
San nan ya bayyana cewa idan matasa suna shiga cikin harkokun kasuwanci, ko shakka babu kasarnan za ta kara samun ci gaba ta kowane fanni.Kuma za a kara samun guraben ayyukan yi musamman ganin cewa idan matasa suka karbi abu, ana cimma gagarumar nasara a cikinsu saboda basirar da Allah Ya ba su.
Daga nan ya bukaci ’yan uwansa matasa da su ci gaba da kasancewa masu bin dokokin kasa da kaucewa duk wani abu da zai iya kawo rashin kwanciyar hankali ga al’umma a dukkanin inda suka samu kansu. Har ila yau, ya ce lokaci ya yi da matasa za su watsar da duk wani abu da zai ba ta masu tarbiyya da zaman kashe wando.
Ya ba da misali da cewa akwai matasa kimanin guda takwas da ke aiki karkashin kasuwancinsa, wanda hakan ya sanya yake fatan ganin ana fadada abin ta yadda za a bude kafofi ga dimbin mutane ba tare da an zura wa gwamnati idanu ba, koda ko bayan an kammala karatu ne.
Matashin dan kasuwar ya kuma bayyana cewa idan har aka rike kasuwanci bisa gaskiya da rikon amana, za a samar da yanayi mai kyau na saye da sayarwa kamar dai yadda ake gani a kasashen da suka bunkasa ta fuskar kasuwanci tun lokaci mai tsawo.