✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai barazanar kai wa Majalisar Kano hari —’Yan Sanda

’Yan sanda sun lashi takobin casa duk masu neman hana zaune tsaye a kan dambarwar rushe sabbin masautun Jihar Kano

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ce akwai barazanar wasu bata-gari na shirin kai wa majalisar dokokin jihar hari a ranar Litinin.

Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka gudanar a cikin daren Lahadi a gidan gwamnatin jihar.

Kwamishinan da sauran jagororin hukumomin tsaron jihar sun kwashe kwanaki uku cikin matsanancin aiki bayan “gyaran dokar masarautu” da majalisar dokokin jihar ta kammala a ranar Alhamis.

A ranar Alhamis din Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar wadda ta soke masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin jihar karkashin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.

Kwamishinan ya ce, “Mun samu sahihan bayanai game da wasu bata-gari da ke kokarin yin ta’addanci a wurare da dama musamman majalisar dokoki da sauran muhimman wurare a Jihar Kano.

“Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa akwai masu niyyar saka wuta a majalisar dokokin jihar Kano.

“Duk wanda ke son gwada kwanji da jami’an tsaro, to ya sani muna da karfin da za mu iya tunkarar sa, mun kammala shirye-shiryen fara sintiri sosai domin gano wuraren da aka sanar da mu cewa ’yan ta’addar suna boye.

“Za mu yi bincike gida-gida domin zakulo duk wanda ke ganin ya fi karfin doka.”

Ya ce, hukumomin tsaro suna so Kano ta zauna lafiya, kuma babu wanda zai iya soke hukuncin da aka zartar.

“Bangaren zartaswa a gwamnati ya cimma matsaya kan batun masarautu, za mu bi abin da dokar ta tanada,” in ji kwamishinan.

Ya kuma bayyana cewa sun samu rahoto kan yadda aka hada wasu kungiyoyi na daba da za a biya su Naira dubu 150,000 domin kai hare-hare a cikin jihar daga daren Lahadi.