✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai barazanar harin ta’addanci da Sallah – DSS

Hukumar tsaron farin kaya, DSS ta ce ƴan ta’adda na shirin kai hare-hare a masallatan idi da wuraren shaƙatawa lokacin Sallah Babba. Kakakin DSS, Dr…

Hukumar tsaron farin kaya, DSS ta ce ƴan ta’adda na shirin kai hare-hare a masallatan idi da wuraren shaƙatawa lokacin Sallah Babba.

Kakakin DSS, Dr Peter Afunanya ne ya sanar da haka a ranar Alhamis.

Don haka ya  buƙaci duk masu kula da wuraren taruwar mutane irinsu kasuwanni da wuraren shaƙatawa da su kai rahoton duk motsin da basu amince da shi ba ga jami’an tsaro.

Ya ce DSS ta ƙwato abubuwa masu fashewa daga hannun waɗanda take zargin ƴan ta’adda ne.

Dr Afunanya ya ce hukumar ta kuma  kama makamai da albarusai daga wurin ƴan ta’adda a kan hanyar Abuja – Keffi cikin jihar Nassarawa.