✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai alfanu a ziyarar Gwamna Badaru Chaina

Mutum ba zai iya hana adawar siyasa ba, amma duk da haka kowa ya san daidai, musamman idan mun yi la’akari da irin alfanun da…

Mutum ba zai iya hana adawar siyasa ba, amma duk da haka kowa ya san daidai, musamman idan mun yi la’akari da irin alfanun da ke tattare da ziyarar Gwamnan Jigawa Badaru kasar Chaina. Gwamnatin Alhaji Badaru Abubakar, daya daga cikin burinta akwai samar wa matasa aikin yi, domin matasa su ne kashin  bayan rayuwa a kowane irin mataki, kuma matasa su ne kashin bayan al’umma. Na san mutanen jiha da sauran ’yan adawa za su so sanin irin dimbin alheran da gwamna ya samo daga kasar Sin. Koma dai mene ne sai a yi duba da idon basira, kuma tarihi shi ne babban alkali. Masu aiki da hankali kamata ya yi su bayar da shawara kan yadda za a ciyar da jihar gaba, amma ba suka mara ma’ana ba.
Dawowar Gwamna Badaru daga kasar Chaina, sai ga wasu jibga-jibgan Turawa na kasar Chaina a cikin manya-manyan  kàtafilun aiki kirar kasar Sin dauke da wasu irin mulmulallun karafa, masu kaifi da masu tsini da kuma masu alamar sanya abu ya yi sumul-sumul, wadanda ake amfani da su wajen yankawa da goge duwatsu ana mayar da su mabul, kai ka ce ba ma Jigawa suka yi irin wadancan mabul ba, domin sai ka rantse da Allah shigowa aka yi da su daga Malesiya ko Japan ko kuma daga Afirika ta Kudu, inda duwatsu suka yi sansani
A gaskiya zuwan Badaru kasar Chaina da wasu ’yan adawa ke yi wa muguwar fassara suke dangantashi da Gwamnatin Saminu Turaki da ta shude, suna bata shi, suna bata gwamnatin da sunan adawa, suna cewa, ‘wai ba zai yi adalci ba. A gaskiya wadanda ke yin adawa da manufar Gwamna Badaru tamkar suna rusa kansu ne da kansu. Domin ba don komai ta fara bayyana a fili cewar adawa ce da gaskiya suke fada ba jama’a ba
Bahaushe ya ce ‘sara da sassaka ba ya hana gamji toho,’ yin maganganu masara ma’ana a rediyo da wadancan ’yan adawa ke yi a kullum suna yawan rubuce-rubucen karya a shafukan jaridun kasar nan, Badaru kyale su ya yi su rusa kansu da kansu. Domin kuwa kowa ya fara fahimta ba su da gaskiya ne, shi ne ya sa suke kalaman batanci. Bahaushe dai ya ce shiru ma maganace.
Kowa ya san an ce ja da baya ba gudu ba ne inji Bahaushe. Na san jama’a wadanda ba su fahimci, inda aka sa gaba a siyasar Jihar Jjigawa ba za su yi mamaki da zarar sabuwar shekara ta kama, sabuwar Gwamnatin Badaru da bude aiwatar da ayyukan raya kasa a cikin manyan birane da karkara, yayin da arziki ya kwararo cikin jihar,  kowa ya samu aikin yi. Mutane za su bambance da barcin makaho, ba sai an fada musu ba. Jama’a na ta kara talauci, ya kamata su sani maganar rashin kudin nan da wasu ’yan adawa suke ta yi, cewar, wai Badaru ya kawo talauci a Jihar Jiigawa, ya kamata su fahimta ba iyaka Jihar Jigawa ba ne ake fama da kuncin rayuwa, ai duk Najeriya ne.
Shugabannin da suka shude su ne suka sanya kasar da jihohi cikin wannan kangi na bakar fatara da ake fama da ita, amma saboda a yanzu su ne shugabanni shi ya sa ake dora musu laifi, su kuma wadancan su Sule Lamido da iyayen gidansa sun ci bulus, kura da sata, jaki da shan bugu.
Mu gode wa Allah subahanahu wa ta’ala. Da yardar Allah komai ya kusa zuwa karshe kamar yadda bincike ya nuna za a dauki matasa sama da dubu 10 aiki a bangaran kamfanin mabul tayil, wandan kamfanin GCC yake share wurin fara aiki a unguwar Fanisau da ke Dutse. Ana sa  ran za a dauki leburori da masu sarrafa injina da masu gadi da likitoci da akawu akawu a farkon farawa mutun 200. Kuma wannan bangare daya ne na ayyukan da gwamnan ya kawo akwai wadanda za su bude a kan sinadarin copper iron da sinadarin hydro wadda ake hadin man fetur da shi da kawolin da kuma tama da ake yin rodi da ita, ga kuma kamfanin sugar da shinkafa, wanda tuni aka fara aikin share filin shuka raken da kamfanin zai fara amfani da shi, da shuka shinkafa, tuni aiki ya yi nisa ba ma ’yan Jihar Jigawa ba, makota daga waje, kamar Kano da Bauchi da Yobe da ma Jamhuriyar Nijar, inda ’ya’yansu da matansu za su amfana da irin alkairan da gwamna ya shigo da su daga kasar Sin
Fara shigowar kamfanonin hakar ma’adanai Jihar domin cigaban jama’ar jihar da ita kanta gwamnatin tarayya, ya fara sauya hannun agogon siyasar jigawa. Saboda yanzu kullum jama’a ba sa komai sai batun sauya shekar siyasa daga PDP zuwa sabuwar jam’iyya mai mulki ta APC, domin sun fara fahimtar inda gaskiya take.