Jam’iyyar APC ta gamu da cikas kan shirinta na fara sayar da fom din takara domin darewa kujerun siyasa a zaben 2023 a ranar Asabar.
Masu neman darewa kan madafun iko a karkashin inuwar jam’iyyar a zaben 2023 dai sun yi cirko-cirko a hedikwtar jam’iyyar ta kasa, ganin cewa ba a fara sayar da takardun ba kamar yadda aka tsara.
- ‘Duk wanda ya sayi fom din takarar APC N100m a bincike shi’
- 2023: ‘Da biyu jam’iyyu suka tsauwala kudin fom din takara’
Wata majiya mai tushe a jam’iyyar da ta nemi a boye sunanta ta ce, “Hakan ya faru ne saboda dan kwangilar da aka ba wa aikin buga takardun bai kawo su ba, watakila ya kawo kafin a gama hutun karshen mako.
“Idan har hakan ta faru, za a iya fara sayar da fom daga ranar Litinin ko Talata.
“Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya na Kasa ne zai yanke shawara kan sabon lokacin.”
To sai dai duk yunkurin ji ta bakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyar APC na Kasa, Felix Morka, bai amsa sakonnin da aka tura mishi ba.
Tsadar fom din takara
Jam’iyyar APC mai mulki dai ta shiga bakin duniya tun bayan da ta sanar da farashin takardun tsayawa takara a zaben 2023.
Farashin Naira miliyan 100 da ta sa wa fom din takarar shugaban kasa da kuma mililyan 50 na kujerar gwamna da dai sauransu ya jawo ce-ce-ku-ce.
Sai dai kuma wannan kari ba a jam’iyyar ba ce kadai; hasali ma, jam’iyyar adawa ta PDP ta kara fashin fom din takara a karkashin inuwarta da sama da kashi 300 cikin 100, idan aka kwatanta da lokacin zaben 2019.
Masu sharhi dai na ganin tsawwala farashin wani salo ne da hana matasa da masu karamin karfi shiga da dama da su wajen neman mukaman shugabanci da na wakilci.
Wasu na ganin duk dan siyasar da ya ware irin makudan kudaden nan ya sayi fom, to babu yadda za a yi ya yi wa jama’a aiki.