Tauraron fim din Indiya, Akshay Kumar ya baje kolin fasaharsa a Dubai. Kamar yadda majiyarmu ta tabbatar, jarumin ba kawai ya tallata fasaharsa ne a kasar ta Larabawa ba, akwai yunkurin da yake na ganin cewa ya mallaki gida na kashin kansa a kasar, kamar yadda takwarorinsa irinsu Shah Rukh Khan da Shilpa Shetty da kuma iyalan gidan Amitabh Bachchan suka yi.
dan wasan ya tabbatar da haka ne ga ’yan jarida, a yayin da ya kai ziyara kasar a farkon makon nan, a lokacin da ya kaddamar da tawagar wasan kwaikwayonsa mai taken ‘Once Upon a Time in Mumbai Dobaara.’ A cikin tawagar tasa, har da fitattun ’yan fim, Sonakshi Sinha da Imran Khan.
A yayin da Akshay ya sauka Dubai, ya samu gayyata ta musamman daga Shaikh Muhammad bin Maktoum bin Juma Al Maktoum a gidansa, inda suka tattauna kan al’amura da dama, ciki har da kudurinsa na sayen gida a Dubai.
“Dubai babban birni ne mai maraba ga baki. A duk lokacin da na kasance a cikinsa, ji nake kamar ina gidanmu.” Inji Akshay, a lokacin da yake tsokaci game da Dubai.
“Wannan ne ma dalilin da ya sanya na yanke hukuncin cewa zan mallaki gida a nan. Hasali ma, a yayin da nake kiciniyar kaddamarwa da baje kolin fasahata, a gefe daya kuma matata Tina tana can tana ta neman gidan da ya dace na saya a birnin.”
Ya kara da cewa: “Ka san akwai Indiyawa da ’yan Pakistan da yawa a nan Dubai. Yanayin birnin mai ni’ima ne da dadin zama. Idan ina cikinsa, ji nake kamar a Indiya nake. A lokacin da nake da zabin zama a wata kasa ba Indiya ba, to Dubai zan zauna har tsawon rayuwata.
Akshay Kumar dai yana auren tsohuwar ’yar fim, Twinkle Khanna kuma suna da ’ya’ya biyu, Aarab da Nitara.”
Akshay Kumar ya baje kolinsa a Dubai
Tauraron fim din Indiya, Akshay Kumar ya baje kolin fasaharsa a Dubai. Kamar yadda majiyarmu ta tabbatar, jarumin ba kawai ya tallata fasaharsa ne a…
