✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AKSAT ta yaye mahaddata 51 a Gombe

A ranar Asabar da ta gabata ce makarantar Academy of Kur’an Science and Tauhid, (AKSAT),  ta Zubair Bn Auwam da Malam Auwal Ahmad Gafakan Akko ya…

A ranar Asabar da ta gabata ce makarantar Academy of Kur’an Science and Tauhid, (AKSAT),  ta Zubair Bn Auwam da Malam Auwal Ahmad Gafakan Akko ya kafa a Gombe ta yaye dalibai 51 da suka haddace Alkur’ani Mai girma a karo na hudu.

Da yake jawabi a wajen taron, zababben Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yaba wa kokarin Malam Auwal Ahmad Gafakan Akko, na kafa makarantar, wanda ya bayyana a matsayin mai taka rawar gani wajen yaye matasa maza da mata mahaddata Alkur’ani.

Alhaji Inuwa Yahaya, ya ce yana alfahari da Malam Auwal Ahmad, kasancewarsa malamin addini kuma dan siyasa da ko a lokacin yakin neman zabensa, ya taka rawar gani.

Zababben Gwamnan  wanda Ciroman Gombe, Barista Zubairu Muhammad Umar ya wakilta, ya taya mahaddatan murna tare da yin kira kan su zurfafa karatunsu wajen fassarar Alkur’anin.

Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III,  ya yaba wa Ustaz Auwal Ahmad Gafakan Akko, ganin yadda ya jajirce a bangaren Alkur’ani, har ya bude makarantar da ta yaye dalibai da dama.

Sarkin, wanda Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam, (JNI) na Jihar Gombe, Alhaji Saleh Danburam, ya wakilta ya jawo hankalin daliban cewa su zama masu aiki da abin da suka karanta saboda duk mahaddaci kamata ya yi a same shi da hali na kamala.

Da yake tsokaci a wajen taron Mai martaba Sarkin Pindiga Alhaji Seyoji Muhammad Ahmed cewa ya yi a shiyyar Arewa maso Gabas an shiga wani hali da ke bukatar  a sake yin dubi a kan matsalar raba maza da mata a makarantun kwana wanda hakan ne ke bai wa masu garkuwa da mutane dama suna sace ’yan mata a makarantunsu.

Sarkin na Pindiga, ya kara da cewa namiji garkuwa ne ga mace don haka a duba wannan lamari da kyau, don sake hade su waje guda domin matan su samu kariya.

Sheikh Adamu Muhammad Dokoro, jinjina wa Malam Auwal Gafakan Akko ya yi kan wannan abin alheri da ya gina a Gombe a wannan lokaci da ake da bukatar matasa su samu ilimi, inda ya ce Allah ne kawai zai biya shi.

Sheikh Adamu Dokoro, ya ce mahaddacin Alkur’ani mutum ne da ya dace a girmama shi, kuma bai kamata a same shi yana aikata abin da bai dace ba.

Malam Auwal Gafakan Akko, ya gode wa jama’a bisa yadda suke ba shi hadin kai wajen tafiyar da makarantar, inda ya ce ba don goyon bayan da yake samu ba da ba abin da zai tafi yadda ya kamata.