✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akalla mutum 15 ke mutuwa a titunan kasar nan Kullum – NBS

Akalla mutum 15 ne suke mutuwa a kullum sakamakon hadarin mota da ke faru a kan titunan kasar nan, hadarin da da aka fi danganta…

Akalla mutum 15 ne suke mutuwa a kullum sakamakon hadarin mota da ke faru a kan titunan kasar nan, hadarin da da aka fi danganta shi ga tukin ganganci da rashin bin dokokin hanya.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ce ta wallafa wannan rahoto a shafinta na Intanet, inda yanzu ake jiran sabon rahoton  da zai tabo yanayin hadduran da suka faru musamman a lokacin bukukuwan da suka wuce.

Bayanan dai suna nuni ne da cewa akan samu haddura ne, sakamakon tukin ganganci da shan barasa ko kayan maye kafin direbobi su hau kan titi inda hakan ya shafi masu shan kwaya don kara kuzari don yin jigilar fasinja ba tare da gajiya ba. Manyan dalilan da Hukumar NBS ta bayyana ba su tabo batun rashin kyan hanyoyi ko rashin magogin gilashi idan ana ruwan sama ba.

Rahoton kuma ya ce Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) takan sanya jami’anta yin aiki a kan tituna ne da rana kawai.

Wata matsalar da ke haifar da hadarin, ita ce ta cin karo da ’yan fashi da kan tilasta direbobi tsayawa ko su nemi banke shingensu don tsira. Kuma hakan kan kare da bude wuta daga miyagun.