Hajiya A’isha Ibrahim dankani lauya ce, kafin ta yi ritaya ta zama darakta a ma’aikatun tarayya 16 da suka hada da ta mata da ta ‘yan sanda da ta kimiyya da fasaha da sauransu. Ta ce burinta a samu canji a Najeriya musamman ma Arewa, kuma ta ce kwalliya da ado ba su ba ne aure.
Tarihina
Sunana A’isha Ibrahim dankani. An haife ni a watan Oktoba, 1962. Ni ‘yar Jihar Kano ce daga karamar Hukumar Dala. Na yi makarantar firamare da sakandare a Saint Luis ta Kano. Bayan haka, sai na tafi Jami’ar Bayero (BUK) ta Kano, na karanta bangaren Shari’a (Law school) na kuma fara aiki a ma’aikatar Shari’a ta Kano. Na yi shekara 10 da su. Daga nan na yi aiki da ma’aikatun tarayya da dama har na zama Darakta a ma’aikatu 16. Ga kadan daga cikinsu: Na fara da ma’aikatar mata ta tarayya (Women Affairs) da ta Kimiyya da Fasaha da ta ’yan sanda da sauransu, na kuma yi aiki da ma’aikatar shugaban kasa (Presidency), inda shekara uku da suka wuce na yi ritaya.
Abin da ba zan manta ba da shi lokacin da nake karama ba
A gaskiya mu ‘ya’yan da za a ce an haife mu da takalma ne ba kamar shugaban kasa Jonathan ya ce an haife shi ba takalmi ba. Muna da gata gwargwadon hali. An rika kai mu makaranta da mota kuma direba ya dawo da mu, mahaifina na cikin tsirarun ‘yan kasuwar Kano wadanda suka ba ilimi muhimmanci a wannan lokacin. Duk da cewa makarantar gwamnati a lokacin na da kyau, amma ba a samu a makarantarta ba. Gaskiya na yi kuruciya mai ban sha’awa. Ba zan manta ba akwai wata fasto mace a makarantarmu, da yake makarantar mishan muka yi a lokacin. Ni da kawata muna tsoransu sosai. Kullum sai sun tambaye mu kirgen da ke bayan littafinmu kuma sukan ce lallai sai mun hardace su (2d1)). In muka shiga aji bayan mun gaida malamanmu sai mu kawo haddar kirgen bayan littafinmu daga farko har zuwa karshensa. Hakan yakan ba ni tsoro har ko a barci nakan yi ba tare da na san ina yi ba. Yana cikin abubuwan da nake tunawa a lokacin da nake karama, babu wani abu illa karatun Muhammadiyya da na boko. Kuma in muka fita da safe, sai yamma muke dawowa.
Shakuwa tsakanin iyaye
Na fi shakuwa da mahaifina saboda mutum ne wanda kowa zai yi sha’awar ya zama mahaifinsa. Ma’ana, ba mahaifi ne wanda kawai zai nemo abinci a ci ba ko ya biya kudin makaranta ba, uba ne da ke cikin rayuwarmu ta kodayaushe. Irin abincin da za mu ci, muna da direban da ke kai mu makaranta. Amma idan 7 saura minti 5 ta yi kuma direba baya nan, baba yana cikin mota yana jira da makulli ya sauke mu a makaranta ko ya tashe mu a barci, ya surka ruwan wanka, kuma yana gasa mana biredi.
Abin da na koya daga mahaifina
Na koyi kasuwanci da kuma neman abin kaina. Domin mutum ba zai dogara da aikin gwamnati ko kwangila ba. Mahaifina na da yakinin cewa in mutum ya yarda a kan Allah Zai yi, zai yi. Kuma haka ne don ba abin da na taba zama na roka da Allah bai ba ni ba. Alhamdulillah. Akwai wata aya da yake yawan karantawa a lokacin yana jinya kafin rasuwarsa. Kuma ayar na magana a kan idan mutum ya yarda da yakinin Ubangiji, zai isar masa komai.
Yadda na hadu da maigidana
Shekara 3 da suka wuce maigidana ya rasu. Kuma ya rasu ne sakamakon ciwon daji. Kamar yadda na fada aikin gwamnati ba aiki ne wanda mutum zai dogara da shi ba. Ni da maigidana mun yi aiki a waje daya, shi ma yana hangen abin da nake hangowa. Kuma tunaninmu yakan tafi daya. A haka muka yi aure.
Farin cikin zama uwa
A gaskiya a lokacin ina karama, kuma daga mun gama makarantar sakandare aure ake mana. Daga nan kuma sai mu ci gaba da karatu a gidan mijinmu. Na tafi jami’a da aurena. Kuma kafin na tafi jami’a na haihu. Ba kawai a yi mana aure mu haihu ba ne mahaifinmu ya tabbata ya ba mu tarbiyya tagari, ya tabbata mun yi karatu. A gaskiya a lokacin ina shekara 17. Ban san me nake yi ba. Domin sai dai in ajiye dana a gida na tafi makaranta.
Abin da nake yi yanzu
Ni lawya ce amma kuma ba na zuwa kotu, aiki da ma’aikatu daban-daban da na yi ne ya sa ban tsaya a fannin shari’a kawai ba. Kamar yadda na ce an koya mana kasuwanci, a shekara uku da muka bar aiki, sai na fara sana’ar mahaifina. Na dauki otel dinsa mai suna dankani Guess Palace guda daya wanda yake Sakkwato. Kuma ina samun biyan bukata daidai gwargwado. Yanzu muna kokarin bude wani a Zariya. Kuma mun hada hannu da wata kawata muka bude Lekki horizon a Legas. Ga harkar sayar da gidaje. Daga nan kuma, sai na bude makarantar Islamiyya, Darul kur’an Islamic Center.
Yadda nake taimaka wa mata
Rayuwar da muka samu kanmu mu ‘yan Arewa a yau na damuna. Har a barcina da tashina, a tafiyata, a hirata da kowa, shi ne abin da nake sa wa a gaba. Kuma duk mutumin da yake da hankali, ya san al’ummarmu ta shiga halin kaka-nikayi. Ba daidai ba ne mu nade hannuwa mu jira wadannsu su ceto mu, komai kankantanr aiki idan aka hada hannu to za a samu gyara. Ba wata al’umma da ke tafiya da ka, da ba ta da jagora, ba ta da shugabanni kuma ba a damu ta ci gaba ba. Wannan su ne matsalolin da ni da mutane muke ganin ya kamata mu kalla. Wannan yana daga cikin dalilin da ya sa muka bude makarantar Darul kur’an ke nan. Mukan zauna mu yi hirar yadda za mu samu mafita a kan abubuwan da suka shafe mu. Kuma ana kallon karatun allo kaskanci ne domin a karkashin bishiya ake yi. Shi ya sa muka bude wannan makarantar kuma ake koyar da Al’kur’ani a Islamiyyar. Muna so a kalli musulunci a kan hanya ta kwarai da gaskiya. Na shiga kungiyoyi biyu wanda za mu iya hada kai da su domin cim ma burinmu masu suna Network for justice da kungiyar arewa. Wanda suke kallon arewa da halin da muke ciki da yadda za a samu mafita. Mukan yi kasuwancinmu kuma a Arewa domin idan ka kawo kasuwanci gida, ’yan gida za su fi amfana da shi kuma da yawansu za su zama ma’aikatar wannan kasuwar.
kalubale a wurin aiki
Fitowar mutum daga Arewa babbar matsala ce. Akwai wannan tunanin irin nasu na cewa, dan Arewa bai kai dan Kudu ba ko a tunani. Saboda haka, duk ma’aikatar da kika je, za ki ga ‘yan Kudu da dama kuma tunaninsu shi ne: ‘yan Arewa ba ku kaimu ba kuma iliminku ma bai kai namu ba don haka ba za ku iya ba”. Sai kin yi kokarin ganar da su cewa ke ma zaki iya abin da ‘yan Kudu za su iya yi. Wanda kuwa da ke ‘yar Kudu ce ba sai kin yi hakan ba. In kin yi magana har ana tambayarki ko ke ‘yar arewa ce wai ya aka yi kika iya Turanci. Akwai ofishin da ake ganin cewa bai dace da mace ba domin kina ‘yar Arewa. Kuma a lokacin da muka shiga aikin mu yara ne. Kuma kai a matsayinka na yaro sai a ga kamar ba abin da ka iya. A matsayinki ta mace dole aiki ya ba ki wahala, idan namiji ne ko ya yi abu ba daidai ba sai a ce nashi ne daidai. Na daya, a shekarunki za a ce baki cancanta ba, a ‘yar Arewanki kuma matsala ne.
Burina
Burina in ga kasar nan ta canza musamman ma Arewa. dan Arewa ya yi tunanin cewa shi bora ne. Da Musa da Abubakar su ne masu gadi. Al’ummarmu ta lalace.
Sirrin zaman aure
Ba wai daga an yi aure, ango amarya shi ke nan ba. Ya kamata mu tsaya mu kalli al’adunmu. Domin shi Musulmi Allah Ya daga shi fiye da kowa. Don musulunci ba harkar sallama ba ce. Harkar rayuwa ce. Ka tambayi kanka. Shin me ya sa aka haife ni? Idan kuma aka haife ni me zan yi? Mece ce makoma? To idan aka kalli wannan, za a ga aure mu’amala ce tsakanin mutane. Ba irin wannan watsewar da muka dauka ba ta Turawa. Kwalliya da ado ba su ne aure ba. Mutane su zamana masu kaunar juna kuma masu tsoron Allah.
Inda na fi sha’awar zuwa hutu
Ina son zuwa Dubai.
Shawara ga matasa
Ina son matasa su yi nazari a kan rayuwa domin tana da karshe. Kuma in abu mai kyau ne ma za a ga sakamako mai kyau in kuma mara kyau ne ma shi ma zai kare. Babu riba a shaye-shaye kuma babu riba a kaskanci, ba riba a bara, babu riba a rashin ilimi, babu kuma riba a rashin sana’a. Babu kuma abin bakin ciki illa a kaskantar da kai. A kuma wulakanta ka amma kuma ya zamana cewa ya shiga zuciyarka a kan cewa ba ka da mafita. Don haka, haka za ka tafi kuma haka za ka dawwama. Ya kamata mu rike rayuwar da idan mutane na abin da babu kyau sai mu ce masu babu kyau. Ya kamata mai kyau ya dawwama a mai kyau.