✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin wata daya matatun man Najeriya ke yi a shekara —Bincik

Fiye da shekara 20 da suka wuce matatar man fetur ta kasa da ke Kaduna take aiki gadan-gadan tare da ba daukacin Arewacin kasar nan…

Fiye da shekara 20 da suka wuce matatar man fetur ta kasa da ke Kaduna take aiki gadan-gadan tare da ba daukacin Arewacin kasar nan tataccen man fetur.

Binciken wakilinmu ya gano cewa a baya kimanin tankokin dakon mai 105 ne suke daukar man fetur da dangoginsa a kullum daga matatar ta Kaduna. Amma a yanzu matatun man Najeriya sun zama kufai don ba a tace mai a cikinsu.
Binciken ya gano cewa, tun hawa mulkin Shugaban kasa mai barin gado Goodluck Jonathan da Ministar Man fetur Diezani Madueke suka janyo tabarbarewar matatun mai musamman ta Kaduna inda a yanzu kusan wata tara ba ta tace danyen man don samar da fetur da dizel da kananzir da man jirgin sama da kwalta da sauransu ba.
Wannan ya janyo yawancin ma’aikatan da ke daffo-daffon da ake tura musu mai daga Kaduna a garuruwan Maiduguri da Yola da Jos da Gusau da Gombe da Kano da Suleja da Minna ba su samu man fetur ba har tsawon shekara biyu a jere.
Mai tsawatawa a kungiyar direbobin dakon man fetur ta kasa (PTD) kuma tsohon shugaban kungiyar na jihar Kaduna Kwamared Gambo Ibrahim Tuge ya zargi Ministar Mai da gurgunta matatar mai ta Kaduna (KRPC) tare da hadin bakin wasu ’yan lelenta da suke samun tallafin man fetur ba gaira ba dalili. Ya yi zargin cewa wadanda suke son a sayar musu da matatar ne suke gurgunta harkar don su ci gaba da shigo da fetur suna cin kazamiyar riba.
Binciken ya kara gano cewa duk man da ake sayarwa a Arewa ana shigo da shi ne ta hanyar dakonsa daga Kudu zuwa Arewa.
“Haka ya sa mai lasisin kamfanin matatar mai na kasa wato NNPC bai iya samun man fetur din. Amma wadanda suke sayarwa a kasuwar bayan-fage kan fiye da Naira 87 da gwamnati ta kayyade da suka sayarwa Naira 130 a kan lita, na yin haka ne saboda suna sayowa ne daga kaasuwar bayan-fage. Lallai akwai kazamiyar almundahana a kamfanin NNPC domin ba a hukunta masu wannan harka sam,” inji Tuge.
Binciken ya kara gano cewa ma’aikatan mai na kasa ba su da wani takamaiman aikin da suke yi a yanzu. Sannan an cika ma’aikatar da ma’aikatan wucin–gadi, yayin da manyan ma’aikatansu ke ta burededen zuwa kasashen waje yin kwas na ba gaira-ba-sabar.
Tsohon Minista a Ma’aikatar Man fetur Alhaji Umaru Dembo ya ce shaida wa wakilinmu cewa “Abu na farko da ya kamaci kowane Ministan Man fetur ya yi, shi ne a zayarci matatun man da duba ma’aikata da ganin hakikanin me ke faruwa ba ya zauna a ofis kamar yadda ake zargin Diezani da yi ba.”
Ya ce “Ana zarginta da shan giyar mulki inda ta rika sassauya manyan daraktoci in sun ja da ita. Da kuma zargin wadanda suke son sayen matatun man fetur din da gurgunta matatun inda inda matatun ke aiki na wata daya kadai a madadin wata 12, don a yi wasu gwanjonsu a araha. Bai dace ba a dauki ma’aikata da yawa ’yan wucin-gadi don a bautar da su.”
Da wakilinmu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Kamfanin Man fetur ta kasa, Mista Ohi Alegbe ta wayar tarho ya ce ba huruminsa ba ne, ya yi magana kan wannan zargi, sai dai a tuntubi jami’in hulda da ’yan jarida na ministar.