✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin Sabunta Kaduna

Kamar yadda alkaluman kidayar shekara ta 2006 suka nuna, hasashen masana ya nuna cewa yawan al’ummar Jihar Kaduna yanzu ya kai kimanin miliyan 9.48 kuma…

Kamar yadda alkaluman kidayar shekara ta 2006 suka nuna, hasashen masana ya nuna cewa yawan al’ummar Jihar Kaduna yanzu ya kai kimanin miliyan 9.48 kuma ana hasahen yawan al’ummar jihar zai karu ya kai kimanin miliyan 12.96 nan da shekara ta 2050. Sannan kamar yadda hasashen ya nuna cewa a cikin mutum miliyan goma da ke Jihar Kaduna, kimanin mutum miliyan 4 ne ke zaune a cikin garin Kaduna. In kuma ana maganar cikin garin Kaduna, ya hada da Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da wani bangare na Karamar Hukumar Igabi da Chikun.

Bugu da kari, hasashen ya nuna cewa Kaduna za ta ci gaba da habaka, yawan al’umma na karuwa inda kashi 55 zuwa 68 cikin 100 na al’ummar da ke zaune a jihar za su kasance suna zaune ne a cikin garin Kaduna. Hasahen nan bai tsaya nan ba, ya alamta cewa sama da mutum miliyan bakwai zuwa takwas suna zaune ne cikin kananan hukumomi hudu a cikin kananan hukumomi 23 da ake da su a jihar, wato kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu da Chikun da kuma Igabi.

Sabon Titin Alkali Road
Sabon Titin Alkali Road

Karuwar yawan al’ummar ya fara haifar da karancin abubuwan more rayuwa da aka tanada shekara da shekaru musamman ma in aka yi la’akari da hasashen da ake cewa nan da wasu shekaru za a samu karuwar jama’a a cikin garin Kaduna da kuma manyan biranen Kaduna da suka hada da Kafanchan da Zariya. Wannan dalili ya sa dole a bukaci karin abubuwan more rayuwa kamar; hanyoyi da gidaje da lantarki da ayyukan yi da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya da asibitoci da sauran abubuwan bukatun rayuwa na yau da kullum in har ana bukatar rayuwa ta inganta.

Sabon Titin Katuru Road
Sabon Titin Katuru Road

La’akari da wadannan matsalolin ya sa Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ta kaddamar da wani shiri na musamman da ta kira “Kaduna Urban Renewal Project,” wato Aikin Sabunta Kaduna. Wannan aiki ne da gwamnatin ta kaddamar domin tunkarar wadancan matsalolin nesa da kusa – a samar da hanyoyi da makarantu da kasuwanni da sauransu. Wasu daga cikin ayyukan da wannan shiri ya kunsa sun hada da:

  1. Yin sababbin hanyoyi da gadoji domin fadadawa da hada sassa daban-daban na garin Kaduna.
  2. Inganta hanyoyin da ake da su a cikin garin Kaduna.
  3. Samar da abubuwan sufuri na zamani
  4. Inganta yadda ake amfani da kasa (gine-gine, wuraren kankanci, wuraren sayar da motoci da kayan gyara da sauransu)
  5. Sanya fitillun kan hanya (Street lights)
  6. Sanya fitulun ba motoci hannu (Traffic lights)
  7. Sanya alamomi na sunayen unguwanni da layuka
  8. Gina kasuwanni da wuraren hada-hada na zamani
  9. Zamanantar da dandalin wasanni na ‘Murtala Skuare’
  10. Yin wuraren wasanni da shakatawa
  11. Yin wuraren kallo na zamani
  12. Samar da wuraren zubar da shara na zamani
  13. Sanya alamomin kan hanya (Road signs)
  14. Samar da kananan shuguna a kan hanyoyi masu amfani da hasken rana (Solar kiosk)

Domin samar da wadannan Gwamnatin Jihar Kaduna ta kulla yarjejeniya da kamfanoni da dama ciki har da Kamfanin CCECC wanda Gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’I ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar a watan Yunin shekarar 2017 domin yin sababbin hanyoyi shida da gadojin sama uku da gadar kasa wanda za ta hada ‘Kabala Costain’ da Barnawa da wata wadda za ta bi ta shatale-talen Lebentis da kuma wata gadar kasa wadda za ta ratsa ta Titin zagaye na Nnamdi Azikwe zuwa Tashar Jirgin Kasa na Rigasa. Sannan da fadadawa da tagwayantar da wasu hanyoyi goma sha biyar (15).

Sabon wurin shakatawa da wasanni na Splash Park (Gamji Gate) Kaduna
Sabon wurin shakatawa da wasanni na Splash Park (Gamji Gate) Kaduna

Sababbin hanyoyin da za a yi

Wasu daga cikin sababbin hanyoyin da za a yi kamar yadda yake a tsarin taswirar ayyukan (master plan), na jihar sun hada da:

  1. Kabala Costain zuwa Aliyu Makama zuwa Barnawa hade da gadar da za ta tsallaka ta kan Kogin Kaduna.
  2. Titin Rabah Road ta Gidan Arewa House ta bi ta Titin Nnamdi Azikwe Bypass da gadar sama (oberhead bridge).
  3. Titin FRCN Road daura da kofar Makarantar FGC zuwa uguwannin ’yan majalisa (Legislatibe Kuarters) a Unguwan Dosa
  4. Akwai sabuwar hanya da za ta tashi daga Titin Nnamdi Azikwe zuwa tashar jirgin kasa da ke Rigasa.
  5. Akwai sabuwar hanya da za a yi daga Titin Umaru Musa ’Yar’aduwa Way” zuwa Hanyar Zagaye ta Gabas (Eastern Bypass mai tsawon kilomita 5.73).
  6. Akwai sabuwar hanya da za a yi da aka kira “Urban Shelter Road” zuwa titin Patrick Yakowa (kilomita 3.5)
Sabon wurin shakatawa da wasanni na Splash Park wato Gamji Gate, Kaduna
Sabon wurin shakatawa da wasanni na Splash Park wato Gamji Gate, Kaduna

Hanyoyin da za a inganta

Baya ga sababbin hanyoyin da za a yi a Jihar Kaduna wadanda an fara wasu da dama, gwamnatin ta zabi wasu tsofaffin hanyoyi a jihar da za ta inganta su ta hanyar fadada su ko tagwayantar da su. Wato wasu za a mayar da hanyoyi na je-ka ka- dawo. Wasu daga cikin wadannan hanyoyin sun hada da:

  1. Tagwayantar da Titin Alkali Road tare da sanya fitullun kan hanya da kuma fitulun ba ababen hawa hannu (kilomita daya). Yanzu haka an kammala aikin hanyar.
  2. Tagwayantar da Titin Yakubu Gowon Way, Asibitin Barau Dikko zuwa Titin Waff Road (kilomita 2.2). Wanna ma an gama.
  3. Fadada hanyar da ake kira Swimming Pool Road, wadda ta fara daga shatale-talen Kwalejin ’Yan sanda (Police Roundabout) zuwa Masallacin Almannar.
  4. Tagwayantar da hanyar Poly Road, wadda ta fara daga Gidan Gwamnati ta bi ta Titin Dutsenma Road zuwa shatale-talen Kasuwar Barci.
  5. Tagwayantar da hanyar da ake kira Dutsenma Road wadda za ta bi ta Gidan Man Shema zuwa Titin Poly Road (kilomita2).
  6. Fadada hanyar da ta tashi daga kofar Gidan Gwamnati ta bi ta Gamagira Road zuwa Nnamdi Azikiwe Bypass (kilomita 3.7).
  7. Fadada Titin Laminu Road da ke Unguwan Rimi, wanda ya fara daga Gidan Man Total zuwa Titin Ramat Road (kilomita 0.9)
  8. Tagwayantar da Titin Rabah Road, wadda ta fara daga Gidan Arewa House zuwa Water Board (kilomita 4.2).
  9. Fadada hanyar da ake kira Kinshasha Road da ke Unguwan Rimi (kilomita 1.6).
  10. Tagwayantar da hanyar da ake kira Katuru Road,
  11. Fadada mahadar hanyar Sultan Road da Isah Kaita Road.
  12. Tagwayantar da Titin Waff Road zuwa NEPA Roundabout zuwa mahadar Essence Junction da kuma fadada mahadar ta Essence.
  13. Tagwayantar da Titin Race Course wanda ya tashi daga Hanyar Independence Way zuwa titin Tafawa Balewa (kilomita 1.2).
  14. Kammala hanyar da ta tashi daga Nasarawa zuwa kamfanin fulawa (Flour Mill).
Ana aza harsashin ginin gadar sama a Titin Ali Akilu, Kaduna
Ana aza harsashin ginin gadar sama a Titin Ali Akilu, Kaduna

A yanzu dai aikin sabunta Kaduna ya kankama ya yi nisa, domin an kammla wasu ayyukan, wasu kuma an yi nisa da farawa, sannan wasu yanzu ake farawa. Misali, an tagwayantar da Titin Katuru Road da kuma Alkali Road. Haka kuma aikin tagwayantar da Titin Waff Road da ya tashi daga shatale-talen NEPA zuwa Mahadar Essence shi ma ya yi nisa.

Bugu da kari, an fara aikin  sabuwar hanya mai tsawon kilomita 5.73 wadda za a yi daga Titin Umar Musa ’Yar’aduwa Way  zuwa Hanyar Zagaye ta Gabas (Eastern Bypass).

Titin Waff Road da ake kan aikinsa
Titin Waff Road da ake kan aikinsa

Ta fannin fitulun kan hanya (Street light) kuma an sanya a  Mahadar Command Junction da Kwanar KADGIS da Mahadar NDA  da Kwanar WAEC da Titin Gwamna Road/ Mahadar Kwalejin Gwamnati da Bida Road/Independence Way da Shehu Laminu Road/Total da Mahadar Fijo da Jabi Road da Titin Legas da Kano Road da kuma Total Malali

Baya ga ayyukan hanyoyi, akwai sabuwar gada babba ta zamani da za a rushe wadda ake da ita a Kawo a yi domin rage cinkoson ababen hawa. Ita ma Kamfanin Mothercat ya fara wannan aiki. Sannan kuma, an fara aikin gadojin sama a Titin Ali Akilu domin saukaka wa mutane wajen tsallake titi.

Cikin sabon wurin shakatawa na Kaduna Centenary Park
Cikin sabon wurin shakatawa na Kaduna Centenary Park

In kuma aka dawo ta fannin samar da wuraren shakatawa da wasanni, an kammala wani sashe na wurin wasanni da shakatawa na Kaduna Centenary Park, wanda a nan ne aka yi bikin murnar shigar sabuwar shekara ta 2020. Haka kuma an kammala wani sashe na wurin wasanni na “Splash Park.”

A bangaren kasuwanni, ginin sabuwar kasuwa ta zamani na Kajuru ya yi nisa. Sannan an aza harsashin ginin sabuwar kasuwa ta zamani a Sabon Garin Zariya –an rushe tsohuwar kasuwar ana gina sabuwa ta zamani.

Kofar sabon wurin shaqatawa na Kaduna Centenary Park
Kofar sabon wurin shaqatawa na Kaduna Centenary Park

Bugu da kari a watan Agusta, 2019, Gwamna El-Rufa’i ya aza harsashin ginin katafariyar kasuwa ta zamani mai suna Galady Mall a kan Titin Waff Road kan zunzurutun kudi Naira biliyan 3.9, wanda wani shiri ne na hadin gwiwa a tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna da wani kamfani mai zaman kansa. Aikin kasuwar yana da sassa daban-daban da suka hada da dakunan silima 3, layin shaguna 48, wurin ajiye motoci sama da 369, hanyoyin tafiya da kafa da sauran abubuwa. Shi ma wannan aiki ya yi nisa.

A takaice dai yanzu ana iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu  game da AIKIN SABUNTA KADUNA domin kowane lungu da sako na garin Kaduna aiki ake yi.

 

Abdullah Yunus Abdullah

[email protected].ng