✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin Hajji da hukunce-hukuncensa (8)

Dabbar daji da madadinta ta gida                          Giwa -Rakumin Tulkumami Jimina- Rakumi Bauna – Saniya Jakin Daji – Saniya Barewa – Saniya Kura – Akuya ko…

Dabbar daji da madadinta ta gida                          Giwa -Rakumin Tulkumami

Jimina- Rakumi

Bauna – Saniya

Jakin Daji – Saniya

Barewa – Saniya

Kura – Akuya ko tunkiya

Yanyawa –  Akuya ko tunkiya

Tantabarar Harami – Akuya ko tunkiya

Kurciyar Harami – Akuya ko tunkiya

Damo – Kima ta abinci ko azumi

Zomo – Kima ta abinci ko azumi

Kurege – Kima ta abinci ko azumi

Tsuntsaye – Kima ta abinci ko azumi

Tantabarar Hillu – Kima ta abinci ko azumi Kwai – Ushurin kimar uwar

Tayi – Ushurin Kimar uwar fara daya

Hafna – Tafi daya na abinci

Alkalai

To, ko da yake an ba da kwatancin dabbobin gida wadanda za a fitar a matsayin dabbobin daji, duk da haka wajibi ne mutum ya je wurin wadansu mahukunta biyu su gaya masa abin da zai bayar. Aikin wadannan mahukunta biyu shari’a ce sosai ba fatawa ta neman ra’ayi ba ce za su ce ga misali. A matsayin dabba iri kaza wadda ka kashe mun hukunta maka a kanka ka ba da dabba iri kaza hadaya ko ka ba da mudu kaza ko ka yi azumi kaza.

Idan mutum ya fidda sakamakon dabbar farauta, ba da an hukunta masa abin da zai bayar ba, sakamakon bai yi ba wajibi ne ya sake yin abin da aka hukunta masa. Mahukuntan nan wajibi ne su zamo biyu ’ya’ya ba bayi ba, baligai, adalai, masana kimar dabbobin daji.

A wajen yin kima za su kula da abubuwa uku: su ne shekarun haihuwa na dabbar daji da kibarta ko ranarta. Don haka za su gaya wa mutun ya ba da dabbar gida kaza, mai kiba ko ramamma. Amma ba za su kula da karancin dabbar ba ko girmanta ko lafiyarta ko kyanta. Wadannan abubuwa hudu da su da rashinsu duka daya tunda ita wannan dabbar ta farauta mushe ce, bai halatta a ci ta ba.

Tantabara da kurciya na cikin Harami ba su bukatar a hukunta wa mutm abin da zai fitar. Domin shari’a ta riga ta tsananta sha’aninsu, shi ne a ba da akuya ko tunkiya dalilin wannan tsanantawa kuwa, don su sun rigaya sun saba da mutane kwarai.

Ziyarar Masallacin Annabi (SAW)

Madina gari ne babba, yana wajen Arewa da Makka. A cikin Madina Masallacin Annabi (SAW) yake, kuma kabarin Annabi da na Sahabi Abubakar da Sahabi Umarul Faruku suna nan a cikin Masallacin nan an kebe su a gefen Gabas na Masallacin. Kaburburan nan uku a jere suke. Kabarin Annabi (SAW) shi ne farko daga Yamma, sa’an nan a Gabas da shi sai kabarin Sahabi Abubakar, sa’an nan na Sahabi Umaru. Ya kamata mu san cewa alkiblar masallatan Madina tana kallon Kudu ne.

Mutum yana tafiya Madina don ya ziyarci Masallacin Annabi Muhammad (SAW) da kuma don ya samu yin salloli a cikin Masallacin Annabi (SAW) domin an ruwaito cewa yin Sallah a Masallacin Ka’aba ko na Madina ko Masjidul Aksa na Baiti Makaddasi a Falasdinu ya fi yin Sallah a wasu wuraren da lada mai yawa. Sauran masallatan duniya kuwa darajarsu daya ce.

Ziyarar kabarin Annabi (SAW) mustahabbi ne, Annabi (SAW) ya ce:

“Man zara ni ba’ada mauti fa ka’annama zara ni fi hayati”

Ma’ana: “Wanda ya ziyarce ni bayan mutuwata kamar ya ziyarce ni ne a halin rayuwata.”

Ga yadda ake yin ziyarar:

  1. An so mutum ya dakata a wajen Madina don ya yi wanka ya sa tufafinsa masu kyau, ya sa turare kuma.
  2. Sa’an nan ya kama hanyar tafiya zuwa Masallaci a kasa yana mai yawaita salati ga Annabi (SAW) a lokacin tafiyarsa, zai yi salatin a cikin zuciyarsa.
  3. Da shigarsa Masallacin an so ya fara da yin Sallah raka’a biyu (Tahiyyatul Masjidi) idan ya halatta a yi nafila a lokacin nan. Idan kuwa yin nafila a lokacin bai halatta ba, sai ya fara da yin ziyara.
  4. Kowace irin Sallah mutum zai yi a Masallacin Madina ta farilla ce ko ta nafila an so ya yi ta a wurin nan da ake kira Raula. Filine a cikin Masallacin wanda ke tsakanin mumbarin liman da Hubbaren Annabi (SAW) shi ake kira Raula.
  5. Idan zai fara ziyara, zai tsaya ya fuskanci kabarin Annabi (SAW) wato bayansa yana kallon alkibla. An ki wato an karhanta ya lika jikinsa ga ginin hubbaren, ko ya taba shi da hannu, ko ya sumbace shi, ko ya zagayo shi da yawo. Abin da ake so shi ne nuna girmamawa ga kabarin nan. Wannan kuwa ana yin sa ta hanyar tsayawa wuri daya cikin kawaici da dan nisa daga kabarin.
  6. Idan ya tsaya a gaban kabarin Annabi (SAW) sai ya ce:

“Assalamu alaika ayyuhan Nabiyyu wa rahmatullahi wa barakatuhu.”

Sa’an nan ya ci gaba da yin salati a gare shi.

  1. Sa’annan ya gurgusa zuwa ta damansa kamar zira’i daya ya tsaya daidai da kabarin sahabi Abubakar (Allah Ya yarda da shi) ya ce:

“Assalamu alaika ya Ababakarin as Siddik wa rahmatullahi wa barakatuhu.”

Sa’an nan ya kara da yi masa addu’a ta alheri.

  1. Sa’annan ya sake gurguwa ta damansa kamar zira’i daya kuma ya tsaya daidai da kabarin Sahabi Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce:

“Assalamu alaika ya Aba Hafsin Umarul Faruk wa rahmatullahi wa barakatuhu.” Sa’an nan ya kara da yi masa addu’a ta alheri.

Koyaushe mutum ya shiga Masallacin Annabi (SAW), zai yi wannan ziyara kamar yadda muka siffanta.

Za a iya samun Imam Ahmad Adam Kutubi (SP) ta: 08036095723