✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Aikin hadama

Wani saurayi ne ya je wajen yarinyarsa, sai ta kawo masa kula ta ce: “Ga abinci nan ka ci.” Sai ya ce mata ya koshi,…

Wani saurayi ne ya je wajen yarinyarsa, sai ta kawo masa kula ta ce: “Ga abinci nan ka ci.” Sai ya ce mata ya koshi, domin sai da ya ci kaji ya fito. Sai ta ce: “To bari in kawo maka ruwa.” Tana fita sai ya buda kular ya ga naman kaji, sai ya yi ta ci. Da ya koshi sai ya buda hularsa ya zuba. Da ta kawo masa ruwa ya sha sai ya ce zai tafi. Yana isa kofar fita sai labule ya jahularsa ta fadi. Sai ga nama na ta zuba, kawai sai ya ruga da gudu.
Daga Saifullahi Sani Aliyu, 08162173625.