Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya NEDC, ta ce za a kashe Naira tiriliyan 31 a gagarumin aikin sake gina yankin tare da fitar da al’umomin daga kangin talauci.
Da yake karin haske, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce Hukumar NEDC da za ta jibinci wannan gaggarumin tsarin na daga cikin bukatun shugaba Muhammadu Buhari, na ganin an farfado da jihohin yankin arewa maso gabashin kasar.
- Abin da magoya bayan United ke cewa bayan lallasa Arsenal
- Jamus ta ware Euro biliyan 65 domin rage wa jama’a radadin rayuwa
Yankin Arewa maso Gabas ya hada da jihohin Adamawa da Bauchi da Borno da Taraba da Gombe da kuma Yobe wanda ya fuskanci koma baya sakamakon ta’asar mayakan kungiyar Boko Haram.
A cewar Sakataren Gwamnatin Tarayyar a zantawarsa da muryar Amurka, yanzu haka NEDC ta hada kai da masu ruwa da tsaki ciki har da Majalisar Dinkin Duniya wajen bincike a kananan hukumomi 121 da ke yankin, a wani mataki na gano hanyoyin da za a bi don cimma wannan manufa.
Hukumar NEDC ta ce tsarin ya kunshi shirye-shirye sama da 500 wadanda za su inganta tare da saukaka ayyukan ci gaba na zahiri da zamantakewar shiyyar da aka ware shekaru 10 don aiwatar da aikin zuwa 2030.
Gwamnar Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa tsarin zai matukar rage wahallahum da mutanan yankin ke fuskantar la’akari da irin ayyukan da aka sa a gaba.
An kiyasta kashe kudin aiwatar da aikin kan kimanin dala biliyan 80, wanda yake kwatankwacin Naira Tiriliyan 31.01 ake sa ran samu daga hadin gwiwar masu ruwa da tsaki da kungiyoyi da kuma kamfanoni masu zaman kansu na ciki da wajen kasar.