✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ahmed Musa ya bude gidan mai a Kano

  A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles da yanzu haka yake bugawa kulob din Leicester City na Ingila…

 

A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles da yanzu haka yake bugawa kulob din Leicester City na Ingila kwallo Ahmed Musa ya bude katafaren gidan sayar da man fetur na kashin kansa mai suna Myca-7 a birnin Kano.

dan kwallon ne da kansa ya jagoranci kaddamar da bikin bude gidan man bayan ya sauka a Jihar Kano daga Abuja.

Ahmed Musa yana daga cikin ’yan kwallon da aka gayyata da suka yi wa Super Eagles kwallo a ranar Asabar da ta wuce a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a Gasar Neman Hayewa Gasar Cin Kofin Duniya da zai gudana a Rasha a tsakanin Najeriya da Zambiya.

A wasan, Najeriya ce ta samu nasara da ci 1 mai ban haushi da hakan ya sa ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a badi a Rasha.  Duk da yake Musa bai buga wasan ba, amma yana daga cikin ’yan kwallon da suka zauna a benchi suna jiran ko- ta-kwana.

Ahmed Musa ne da kansa ya sanar da labarin bude gidan man nasa a Kano a shafin zumuntarsa na yanar gizo, inda hotonsa ya nuna yadda yake zuba wa wani mai Keke-Napep mai a gidan man.

Idan za a tuna, a watanni baya Ahmed Musa ya bude wata katafaren Cibiyar Koyon Wasanni da aka kiyasta kudinta a kan Naira Miliyan 500 a birnin Kano a matsayin daya daga cikin hanyoyin da yake samun kudin shiga

dan kwallon ya ce yana zuba jari ne a bangarori daban-daban don ya samu abun dogaro da kai idan ya yi ritaya daga buga kwallon kafa.