Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta gudanar da taro a Jihar Katsina a ranar Litinin da ta gabata a ci gaba da tattaunawa domin kawo karshen hare-haren ’yan bindiga a yankin. Taron wanda ya samu halartar gwamnoni 11 cikin 19 na Arewa, tattaunawar ta zartar da yi wa ’yan bindiga afuwa, idan suka ajiye makamai kuma suka tuba daga kisan kare-dangi da suke yi wa al’ummar yankin.
’Yan bindiga da masu satar mutane don amsar kudin fansa da barayin shanu sun hargitsa Arewa maso Yammacin kasar nan. Koda ya ke Jihar Zamfara ta fi sauran jihohin yankin fuskantar wannan matsala, yayin da a cikin watan Agustan bara gwamnatin jihar ta fitar da sanarwar akalla sama da mutum 3000 sun rasa rayukansu sannan kauyuka da dama sun salwanta daga doron kasa. Sannan batagarin suna cin kasuwarsu a sassa daban-daban na yankin kamar Jihar Sakkwato da Kebbi da Katsina. Sannan a cikin wannan shekara lissafin ka iya karuwa, tunda an kai hare-hare a cikin shekarar, sannan an yi asarar rayuka da dama.
Hakazalika a cikin wata sanarwa da Majalisar Dinkin Duniya bangaren kula da ’yan gudun hijira (IOM) ta fitar a cikin watan Yunin bana ta ce mutanen da suka rasa matsugunansu a dalilin hare-haren ’yan bindiga sun kai kimanin dubu 16 da 257 a Jihar Katsina kawai, sannan a Jihar Sakkwato akwai kimanin mutum dubu 12 da 527, sai mutum dubu 38 da 113 an tilasta musu barin gidajensu a Jihar Zamfara. Kananan hukumomi 13 cikin 14 da jihar ke da su suna cikin fargabar mahara, a rahotan na (IOM).
Sakamakon hare-haren ’yan bindiga mutane sama da dubu 20 daga Arewa maso Yammacin Najeriya sun ketara zuwa Jamhuriyar Nijar. Rahoton ya ce “Mafiya yawan mutanen sun isa garuruwan; Madarounfa da Gidan Rumji da Gidan Sory da Gabi da kuma N’Gnelwa da ke Jihar Maradi a Jamhuriyyar Nijar.”
Abin takaicin shi ne yanayin da wadanda suka rasa matsugunansu suke ciki akwai firgici. Rahoton ya ci gaba da cewa, “Suna cikin rashin isasshen abinci a cikin sansanin ga rashin tufafi ga yara kanana da tsofaffi, sannan har yanzu babu wani tanadi da gwamnati ta yi na kula da sansanin.”
Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya ta yi mi’ara koma-baya a kan afuwa ga ’yan bindiga sakamakon halin ni-’yasun da wadanda rikicin ya rutsa da su suka shiga .
A wata takardar bayan taro da Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya karanta wa ’yan jarida ya ce Fulani makiyaya da ’yan banga dole ne su daina yawo da makamai cikin jama’a, musamman cikin kasuwanni. Ana umartar su da su ajiye makamansu kamar yadda yake a kunshe cikin yarjejeniyar shirin afuwa ga maharan.
Ya ce “Makiyaya da danginsu a kyale su, su rika shiga kasuwanni da wuraren ibada da kuma sauran al’amuran yau da kullum na rayuwa, amma ya kasance ba sa dauke da makamai a yayin mu’amalarsu da jama’a kuma su zauna da kowa lafiya. Wadanda aka sace wa shanu kuma za a maido musu da su, ko dai ta hanyar gwamnati ko kuma ta bangaren Kungiyar Fulani Makiyaya ta Meyyati Allah. Sharuddan tubar ’yan bindigar sun kunshi; ’yan-sakai (kato-da-gora) su ajiye makamansu da kuma harsasan da suke da su sannan su saki wadanda suke tsare dasu.”
Mun yaba wa yunkurin da gwamnoni suka yi domin samar da tsaro ta hanyar dakile hare-haren ’yan bindigar. Abin karfafa gwiwa ne kwarai da gaske a ce Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya Adamu Mohammad, ya halarci tattaunawar kuma ya yi alkawarin duba yarjejeniyar da aka yi a cikin wata guda domin mara mata baya. Sai dai ba wannan ne karo na farko da aka yi irin wannan yarjejeniyar da ’yan bindiga a tsakanin gwamnati da ’yan bindigar ba amma a karya daga baya. Abin da muke cewa a kan wannan yarjejeniyar shi ne lallai gwamnoni su sa ido sosai a kan duk wanda ya karya wannan yarjejeniyar a tabbatar an tsare shi kuma an gurfanar da shi sannan a yanke masa hukunci. Misalin yarjejeniyar da aka yi a Zamfara ta haifar da alfanu kadan, koda yake hakan bai hana a kai hare-hare a wasu wuraren ba. Kowace rana sai ka ji labarin kai hare-hare a bangarorin jihar.
Saboda haka ya zama wajibi ga gwamnoni da Rundunar ’Yan sanda su yi wani tanadi wanda zai kasance idan hagu ta kiya sai a koma dama, ma’ana; idan yarjejeniyar ba ta yi tasiri ba, to a shirya wata hanyar ta daban ba sai lokacin wata tattaunawa ya zo ba, domin tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin jama’a.