Tsohon kyaftin din tawagar ’yan wasan Super Eagles, Jay-Jay Okocha, ya ce Najeriya za ta iya lashe kofin nahiyar Afrika da ake buga wa a kasar Kamaru.
Ya ce Najeriya ta dawo da karkashinta da kuma sanya tsoro a zukatan abokan hamayya, bayan doke kasar Masar da Sudan da ta yi.
- Kotu ta tsare shi saboda satar katin ATM din makocinsa
- Hambararren Shugaban Guinea, Alpha Conde, ya tafi Dubai neman lafiya
“A dukkan wasannin biyu da Super Eagles ta fafata, ta nuna bajinta kwarai, musamman yadda ’yan wasan gabanta ke nuna yunwar zura kwallo a raga.”
Ya ce sabon salo da jajircewa da tawagar ’yan wasan ta fito da shi, ya sanya tsohon dan wasan cewa tawagar ganin za ta iya lashe gasar.
A shekarun baya karkashin kwallon Super Eagles ya dakushe, wanda hakan ya kawo koma baya da abun kunya wajen gaza shiga gasar kwallon duniya da kuma nahiyar Afirka da aka yi a baya.
Hakan ya sanya Najeriya zama ta 124 a jerin kasashen duniya da ke murza kwallo a fadin duniya.
Wasannin biyun da Najeriya ta yi nasara, ba iya sauya salonsu kawai ya yi ba, ya yi tasiri wajen sabunta soyayyarsu ga magoya bayansu.
“Abokan hamayya sun fara tsoronmu. Yanzu mun yi nasara a wasanni biyu, ina tunanin za mu zamo abun tsoro ga duk kasar da ta hadu da mu kuma za mu iya lashe gasar,” kamar yadda Okocha ya bayyana wa ESPN.