✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON 2021: Moroko ta yi waje da Malawi daga gasar nahiyar Afirka

Moroko ta wuce zuwa zagaye na gaba bayan samun nasara akan Malawi.

A ci gaba da gasar cin kofin nahiyar Afrika, kasar Moroko ta samu nasarar zuwa zagaye na gaba, bayan ta doke tawagar ’yan wasan kasar Malawi da ci 2-1.

Dan wasan Malawi, Mhango je ya fara jefa wa tawagarsa kwallo a minti na takwas da fara wasa.

Kafin zuwa hutun rabin lokaci, dan wasan gaban Moroko, El-Neysri ya warware kwallon a minti na 45.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci an ci gaba da barje gumi, inda dan bayan kungiyar kwallon kafa ta PSG da kasar Morocco, Ashraf Hakimi ya jefa kwallo a minti na 70, daga bugun tazara.

Kasashen biyu dai sun gwabza wasan ne a filin wasa na Ahmadou Ahidjo da ke kasar Kamaru, wanda a nan ake gudanar da gasar.

%d bloggers like this: