✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON2021: Dalilai 3 da suka sa aka yi waje da Najeriya

Tawagar Super Eagles ta taka rawar gani a gasar AFCON2021.

Tawagar ’yan wasan Najeriya ta Super Eagles dai ta taka rawar gani a wasannin da ta buga a matakin rukuni na gasar cin kofin Nahiyar Afirka, wanda hakan ya ba ta damar lashe wasanni uku tare da hada maki tara.

Ficewar Super Eagles a zagaye na biyu na gasar wacce yanzu haka take gudana a kasar Kamaru, ya ba mutane da dama mamaki.

Sai dai masu sharhi kan sha’anin wasanni na ganin wadannan dalilai uku, su ne suka jawo rashin nasarar Super Eagles a hannun kasar Tunusiya, da ci daya mai ban haushi.

1. Rashin kwarewa daga mai horarwa:

Da dama na ganin Augustine Eguavoen bai nuna kwarewa da gogewa ba wajen zaben ’yan wasan da suka kara da kasar Tunusiya ba.

Eguaveoen, ya yi amfani da Simon Moses wajen ganin ya haifar wa ’yan wasan bayan Tunisiya matsala a yayin wasan, amma sai aka yi rashin sa’a suka rufe shi ba tare barinsa ya yi wani katabus ba.

2. Matsalar mai tsaron raga:

Wasu mutanen da dama kuma na gani amfani da Maduka Okoye da kocin ya yi a matsayin mai tsaron ragar shi ma ya taka muhimmiyar rawa a rashin nasarar.

Galibi dai ana ganin Madukan ba shi da wata kwarewa fiye da Francis Ozoho wanda shi ne ya ke tsare raga kafin sallamar Gernot Rohr.

Kazalika, wasu na ganin kwallon da aka zura wa Najeriya akwai laifin Maduka Okoye, wanda zai iya tureta kafin ta shiga raga.

3. Canjin da bai dace ba:

A lokacin da Tunisiya ta zura wa Najeriya kwallo, kocin ya maye gurbin dan wasa Iheanacho da Iwobi, wanda ya samu jan kati bayan shigarsa filin wasan da minti biyar.

Har wa yau, ana ganin kocin ya nuna rashin kwarewa wajen kasa amfani da kaftin din tawagar, Ahmed Musa.

Musa ya buga wasa daya ne kacal a cikin wasannin rukuni, shi ma a canji ya shigo, sai kuma a wasan da Tunisiya ta cire Najeriya, ya shigo filin wasa saura minti uku a tashi daga wasan.