✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON: Yadda alkalin wasa ya hura tashi lokaci bai yi ba

Wane ne alkalin wasan da ya hura tashi alhali lokaci bai yi ba?

A ranar Laraba da ta gabata ce aka samu rudani bayan alkalin wasa ya hura tashi lokaci bai karasa ba.

Rafare Janny Sikazwe dan kasar Zambiya ne ya yi alkalancin wasan tsakanin Tunisiya da Mali, inda ya hura tashi a minti 85 da dakika 13.

Super Cup: Real Madrid ta doke Barcelona da 3-2 a Saudiyya

Ana cikin rudanin ne, har kocin Mali Mohamed Magassouba ya zauna zai fara zantawa da manema labarai, sai wani ya shigo ya ce masa ya dawo an ce a zo a ci gaba da wasan.

’Yan wasan Mali sun dawo, amma na Tunisiya suka ki dawowa, wanda hakan ya sa rafaren ya sake hura tashi.

Mali ce ta doke Tunisiya a wasan da ci daya da nema.

– Wane ne Janny Sikazwe? –

Ganin lamarin ya tayar da kura, sai mutane suka yi ta cewa rafarin ba kwararre ba ne.

Hakan ya sa Aminya ta gudanar da bincike, inda ta gano cewa yana cikin kwararun rafare a  nahiyar Afirka.

Sikazwe yana cikin alkalan wasa da Hukumar FIFA ke amfani da su a wasannin duniya tun a shekarar 2007, inda ya yi alkalancin manyan wasannin na duniya.

Daga cikin manyan wasannin da ya yi alkalanci akwai Gasar Zakarun Afirka da Gasar Kofin Duniya ta Kungiyoyi wato Club World Cup da Gasar Kofin Duniya.

Shi ne ya yi alkalancin wasan karshe na Gasar Club World Cup da aka buga tsakanin Real Madrid da Kashima Anters a shekarar 2016.

Sannan shi ya yi alkalancin wasan karshe na Gasar Cin Kofin Afirka na shekarar 2017 tsakanin Masar da Kamaru.

%d bloggers like this: