Dan wasan Everton da Najeriya, Alex Iwobi ya sha alwashin cewa tawagar Najeriya ta Super Eagles za ta dauki fansa kan rashin nasarar da ta yi 1-0 a gida a hannun Guinea Bissau a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Afirka a ranar Juma’a.
Dan wasan Guinea Bissau, Mama Balde ne ya ci wa tawagar kasarsa kwallo daya tilo ta wasan, kwallon da ta makale kenan har sai da aka tashi.
- ’Yan Boko Haram 51,828 sun mika wuya — Irabor
- Bayern Munich ta nada sabon koci bayan sallamar Nagelsmann
Iwobi, wanda ke wasa a gasar Firimiyar Ingila ya ce ya zama wajibi su mayar da martini dangane da wannan ci da Guinea Bissau ta yi musu.
Ya sha alwashin cewa za su kara azama a haduwarsu ta biyu, yana mai neman goyon bayan magoya bayan tawagar ta Super Eagles don cimma haka.
Da wannan sakamakon Guinea Bissau ta koma ta daya a rukunin farko da maki bakwai, bayan da ta ci Super Eagles da cin Sao Tome da canjaras da Saliyo.
Super Eagles ta koma ta biyu da maki shida, bayan nasara a kan Saliyo da Sao Tome.
An dai yi wasa na uku-uku a rukunin farko don neman gurbin shiga babbar gasar kwallon kafa ta Afirka da za a yi a Ivory Coast a 2024.
Ranar Laraba Saliyo da Sao Tome suka tashi wasa 2-2 a daya karawa ta uku a rukunin farko.
Ranar Litinin 27 ga watan Maris Super Eagles za ta ziyarci Guinea Bissau, domin buga wasa na hur-hudu a rukunin farko.
Ita kuwa Sao Tome za ta karbi bakuncin Saliyo ranar Lahadi 26 ga watan Maris.
Guinea-Bissau na da maki 7, Najeriya 6, Sierra Leone 2 kana Sao Tome da Principe na da maki 1 a teburin wannan fafutukar neman cancantar zuwa AFCON ta 2024.