Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF ta sanar da jerin ’yan kwallo 28 da ta gayyata da za su buga mata wasanni a gasar AFCON ta badi da za a fafata a kasar Kamaru.
Daga cikinsu akwai Ahmed Musa da Kenneth Omeruo wadanda ke cikin ’yan wasan kasar a shekara ta 2013, lokacin da Najeriya ta lashe gasar.
NFF ta sanya dan wasa Victor Osimhen, dan kasar da ke buga wa kungiyar Napoli ta Italiya a cikin ’yan wasan da za su kare mata mutunci a fafatawar da za a yi da ita a gasar nahiyyar Afirka ta AFCON.
Victor Osimhen na cikin hutunsa na watanni uku a Napoli ne bayan wani rauni da ya samu a watan Nuwamba a fuskarsa.
Amma tun a farkon makon nan aka gan shi yana atisaye, sannan ya wallafa cewa yana fatar zai shiga cikin ’yan wasan da za su buga wa Najeriya a gasar ta AFCON wace ake sa ran gudanarwa a watan gobe na Janairu a kasar Kamaru.
Kelechi Nwakali, Sadiq Umar na kungiyar UD Almeria da ke Sifaniya da dan wasan kungiyar Orlando Pirates a Afirka ta Kudu, Olisa Ndah, na daga cikin ’yan wasan da gayyatarsu ta zamo abin mamaki, inda kuma aka zabi dan wasan cikin gida guda tal, John Noble wanda ke murza leda a kungiyar Enyimba.
Wannan dai shi ne karo na 19 da Najeriya za ta haska a gasar AFCON da ake bugawa duk bayan kowace shekara biyu.
Najeriya ta shiga gasar karon farko da aka buga a shekarar 1963 a kasar Ghana, inda tun ba a je ko’ina ba aka fatattake ta a matakin wasannin rukuni saboda rashin katabus.
Alkaluma na tarihi sun bayyana cewa Najeriya ta lashe gasar AFCON sau uku da suka hada da wadda ta karbi bakunci a shekarar 1980, Tunisia a 1994 da kuma wadda aka yi a Afirka ta Kudu a shekarar 2013.
Karo na karshe da Najeriya ta haska a gasar ita ce wadda aka yi a kasar Masar a shekarar 2019 inda ta kare a matsayi na uku.
A ranar 11 ga watan Janairun 2022 ce tawagar ta Super Eagles za ta fara wasanta da tawagar kasar Masar a filin wasa na Roumde Adjia da ke garin Garoua a Kamaru.
Bayan kwana hudu kuma ’yan wasan na Super Eagles za su barje gumi da tawagar Falcons of Jediane ta Sudan inda kuma a ranar 19 ga watan Janairun za su yi karon batta da Djurtus wato tawagar kasar Guinea-Bissau.
A yanzu dai tsohon kyaftin din Najeriya Augustine Eguavoen ne kocin da zai jagoranci tawagar Super Eagles bayan sallamar Gernot Rohr da aka yi wanda ya shafe shekara biyar yana aikin horas da ’yan wasan na Najeriya.
Dukkanin ’yan wasan da aka gayyata ana sa rana za su iso sansaninsu da ke Abuja a ranar 29 ga watan Disamban 2021, yayin da kuma ’yan wasan da ke Birtaniya ake sa ran isowarsu a ranar Litinin, 3 ga watan Janairun 2022.
Ga jerin sunayen dukkanin yan wasa 28 da aka gayyata da kuma kungiyoyin da suke taka leda:
Masu tsaron raga: Francis Uzoho (AC Omonia, Cyprus); John Noble (Enyimba FC, Najeriya); Daniel Akpeyi (Kaizer Chiefs, Afirka ta Kudu); Maduka Okoye (Sparta Rotterdam, The Netherlands)
’Yan wasan baya: Chidozie Awaziem (Alanyaspor FC, Turkiyya); Kenneth Omeruo (CD Leganes, Sifaniya); Leon Balogun (Glasgow Rangers, Scotland); William Ekong (Watford FC, Ingila); Olaoluwa Aina (Torino FC, Italiya); Jamilu Collins (SC Paderborn 07, Jamus); Abdullahi Shehu (AC Omonia, Cyprus); Zaidu Sanusi (FC Porto, Portugal); Olisa Ndah (Orlando Pirates, Afirka ta Kudu)
’Yan wasan tsakiya: Frank Onyeka (Brentford FC, England); Joseph Ayodele-Aribo (Glasgow Rangers, Scotland); Wilfred Ndidi (Leicester City, England); Chidera Ejuke (CSKA Moscow, Rasha); Kelechi Nwakali (SD Huesca, Sifaniya)
’Yan wasan gaba: Ahmed Musa (Fatih Karagumruk, Turkiyya); Samuel Chukwueze (Villarreal FC, Sifaniya); Victor Osimhen (Napoli FC, Italiya); Moses Simon (FC Nantes, Faransa); Sadiq Umar (UD Almeria, Sifaniya); Taiwo Awoniyi (Union Berlin, Jamus); Odion Jude Ighalo (Al-Shabab Riyadh, Saudiyya); Alex Iwobi (Everton FC, Ingila); Kelechi Iheanacho (Leicester City, Ingila); Emmanuel Dennis (Watford FC, Ingila)