✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON 2021: Najeriya ta yi wa Masar ci 1 mai ban haushi

Iheanacho ya zura kwallon ne minti 30 da fara zagayen farko na wasan da ya gudana a kasar Kamaru.

Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta yi wa kasar Masar ci daya mai ban haushi a wasansu na farko a Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta bana.

Najeriya ta zura wa kungiyar Pharaohs ta kasar Masar ci daya a raga ne ta hannun dan wasanta, Kelechi Iheanacho.

Iheanacho ya zura kwallon ne a bayan minti 30 da fara wasan da ya gudana a kasar Kamaru.

Najeriya da kasar Masar na Rukunin D na gasar da aka fara gudanarwa a karshen mako.