✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON 2021: Najeriya ta tsallake zuwa zagaye na biyu 

Ta samu nasarar ne bayan lallasa Sudan da ci 3-0.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta lallasa takwararta ta Falcons of Sudan da ci uku da daya a wasa na biyu na Gasar Cin Kofin Afirka.

Samuel Chukwueze ne ya zura wa Najeriya kwallo na farko a minti uku da fara wasa, sannan Taiwo Awoniyi ya kara a minti na 45, sannan Simon Moses ya kara a minti 46.

Sudan ta ci dayan ne ta hanyar bugun fanareti bayan Ola Aina ya taka kafar dan wasan Sudan amma ba a gani ba, sai daga baya ne rafare ya duba na’urar VAR sannan ya bayar, inda dan wasan Sudan Walieldin Khedr ya sayar da golan Najeriya.

Da wannan nasarar, Najeriya ta lashe wasa biyunta na farko, wanda hakan ya sa ta tsallake zuwa zagaye na biyu na gasar tun kafin wasanta da kasar Guinea-Bissau.