✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

AFCON 2021: Najeriya ta doke Guinea-Bissau a wasan karshe na rukuni

A dayan wasan rukunin na D, Masar ce ta doke Sudan da ci daya da nema.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta doke takwararta ta Guinea-Bissau da ci biyu da nema a wasan karshe na rukunin D na Gasar Cin Kofin Afirka.

Dan wasan Najeriya Sadiq Umar ne ya zura kwallo na farko a minti na 56, sannan Troost-Ekong ya zura na biyu a minti na 75.

A dayan wasan rukunin na B, Masar ce ta doke Sudan da ci daya da nema.

Da wannan sakamakon, Najeriya ce ta farko a rukunin na D da maki 9 bayan ta lashe duka wasa uku da ta buga.

Sannan Masar Ke biye mata da maki 6 bayan nasara biyu da ta samu a wasa uku.

Domin karanta yadda ta kaya dalla-dalla a wasan, a ziyarci wannan shafi AFCON 2021-2022: GUINEA-BISSAU DA NAJERIA