✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AFCON 2021: Najeriya ta yi wa Masar ci daya mai ban haushi

Super Eagles ta Najeriya ta doke takwararta ta Masar da ci daya da nema a wasan farko na rukunin D na Gasar Cin Kofin Afirka…

Super Eagles ta Najeriya ta doke takwararta ta Masar da ci daya da nema a wasan farko na rukunin D na Gasar Cin Kofin Afirka da ke wakana a Kamaru.

Dan wasan Leicester City ta Ingila, Kelechi Iheanacho ne ya zura kwall a ragar Masar tun a zagaye na farko na wasan wanda ya wakana a filin wasa na Roumde Adjia.

Babban dan wasan Masar, Mohammad Salah bai ji da dadi ba a wajen ‘yan wasan bayan Najeriya, inda suka hana shi sakat.

Tarihi

A yanzu a tarihin wasa 20 da aka buga a tsakanin kasashen guda biyu, Najeriya ta lashe guda tara, Masar ta lashe biyar, sannan aka yi kunnen doki a wasa biyar.

Ga yadda ta kaya nan a wasan daki-daki