✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adon nuna dagawa

Ta yiwu adawa ce ta sanya Gwamnatin Tarayya ta yi hanzarin nesanta kanta daga odar da ta yi na sayen na’urar kwamfutar iPhone ta zinariya,…

Ta yiwu adawa ce ta sanya Gwamnatin Tarayya ta yi hanzarin nesanta kanta daga odar da ta yi na sayen na’urar kwamfutar iPhone ta zinariya, don murnar zagayowar bikin ’yancin kan Najeriya karo na 53 da za a gudanar wata mai kamawa. Duk da haka rahotanni sun tabbatar da hujjar da ke nuni da gaskiyar lamarin. Shafukan sadarwar intanet sun cika da ra’ayoyin mutane kan labarin wannan oda da aka bayar a makon da ya wuce.
Jaridar Birtaniya ta The Independent, ta ruwaito daga bakin wani jami’i, wanda shi ne shugaban Kamfanin sarrafa zinariya na Gold and Co, Amjad Ali, wanda ya yi bayanin nagartar kamfaninsa da ke Dubai, kan kwarewarsa wajen samar da kayayyakin kyaututtukan alfarma. Labarin jaridar ya ruwaito daga bakin Mista Ali, inda ya yi nuni da shirin da kamfaninsa ke yi na samar da kayayyakin da Gwamnatin Najeriya ta saya, wato na’urorin iPhone na zinariya har guda 53 a kan farashin Naira miliyan 700. Kodayake Mista Ali bai bayyana lokacin da za a kawo wadannan kaya ba, ko kuma hukumar da ta kulla cinikin da kamfaninsa, ya bayyana siffar yadda na’urorin za su kasance, wadanda suka hada da dawakai da mikiyar tambarin Najeriya, wadanda za a tabbatar siffarsu ta fito a jikin na’urorin.
Wannan dan kasuwa ya yi amfani da wannan damar domin ya tallata kwarewar kamfaninsa a harkar hada-hadar kasuwanci, ba tare da la’akari da tayar da jijiyar wuyan da kalamansa za su haifar a kasar nan  da ke fafutikar yaki da cin hanci da rashawa, da kokarin gyaran tsarin ilimi, tare da dimbin matsalolin da suka zame wa kasar manyan kalubale. Baa bin mamaki ba ne ganin cewa ’yan Najeriya sun soki lamirin wannan almubazzaranci da ya bayyana karara. Sai dai Minista Yada Labarai, Mista Labaran Maku, ya yi hanzarin karyata kalaman Mista Ali, sannan ya karyata cewa akwai hannun Gwamnati a cikin wannan lamari.
Mista Maku ya bayyana cewa Fadar Shugaban ba ta da hannu a cikin lamarin. Daga bisani kamfanin ya fito da sanarwar janye kalaman, inda ya bayyana cewa ba ruwaito kalaman Mista Ali daidai ba. Domin bayani kawai ya yi kan yadda za a zayyana tambarin Najeriya a kan na’urorin. Sai kawai cikin hanzari kamfanin ya bayyana cewa wannan odar na’urorin iPhone wani dan Najeriya ne ya bayar da ita, kuma baya son a ambaci sunansa.
Gwamnati ce kadai ke da ikon amfani da tambarin Najeriya bisa tanadin doka. Wannan sanannar gaskiya ce, don haka masu aikata ayyukan zamba cikin aminci ke samun nasara idan suka yi amfani da tambarin Najeriya, a irin almundahanar da suke shiryawa, ta hanyar yaudara wajen gabatar da takardun hukuma. Idan har mutane masu zaman kansu za su iya sanya a kera musu kayayyaki ko na’urori masu dauke da tambarin Najeriya ba tare da izinin gwamnati ba, don haka wannan mummunan laifi ne da ya kamata a udanar da bincike a kai. Lallai gwamnati ta sa a gano kowane mutum ne ke da hannu  ta hanyar la’akari da damuwar al’umma kan wannana bin kunya, tamkar dai yadda Mista Maiku ke nuni da hakan. Akwai bukatar ’yan sanda su binciki wannan cinikin kaya, a kuma gano hakiknain manufar yin hakan. Nuna halin ko in kula daga hukumomi ke yi, zai sanya  masu shakku (gaskiyar gwamnati) sun tabbatar da cewa akwai ma sauran bayanai a kan al’amari fiye ma da abin da aka ji, kafin a gani a zahiri.
Najeriya na dimbin hamshakan masu dukiya, wadanda suka himatu wajen tallafa wa marasa galihu, kuma babu daya daga cikinsu da zai karyata cewa yana kashe kudi ko wane boyayyen mutum ne ya yi wannan ciniki? Ko wane ne ya yi shirin sarayar da Naira miliyan 680 don murnar bikin zagayowar ’yancin Najeriya, sai ya fito ya yi alfahari da gudunmuwarsa, ba tare day a boye gaskiyar lamari ba.
Damuwar masu mu’amala da shafukan sadarwar intanet ta tabata, duk da cewa babu hujja a kan haka, tunda a irin wannan lokaci, a na zargin gwamnati na da hannu wajen odar kayayyakin. Hukumomin gwamnati, musamman wadanda ke samar da kudi tsagwagwa, sun saba sayen kyaututtukan alfarma masu tsada, don bai wa bakin kasashen waje. Hakki ya rataya akan hukumomi su shawo kan wannan al’amari, ta hanyar bayyana mutumin da ke hankoron samar wa kasar nan wadannan kayayyaki.Ta yiwu adawa ce ta sanya Gwamnatin Tarayya ta yi hanzarin nesanta kanta daga odar da ta yi na sayen na’urar kwamfutar iPhone ta zinariya, don murnar zagayowar bikin ’yancin kan Najeriya karo na 53 da za a gudanar wata mai kamawa. Duk da haka rahotanni sun tabbatar da hujjar da ke nuni da gaskiyar lamarin. Shafukan sadarwar intanet sun cika da ra’ayoyin mutane kan labarin wannan oda da aka bayar a makon da ya wuce.
Jaridar Birtaniya ta The Independent, ta ruwaito daga bakin wani jami’i, wanda shi ne shugaban Kamfanin sarrafa zinariya na Gold and Co, Amjad Ali, wanda ya yi bayanin nagartar kamfaninsa da ke Dubai, kan kwarewarsa wajen samar da kayayyakin kyaututtukan alfarma. Labarin jaridar ya ruwaito daga bakin Mista Ali, inda ya yi nuni da shirin da kamfaninsa ke yi na samar da kayayyakin da Gwamnatin Najeriya ta saya, wato na’urorin iPhone na zinariya har guda 53 a kan farashin Naira miliyan 700. Kodayake Mista Ali bai bayyana lokacin da za a kawo wadannan kaya ba, ko kuma hukumar da ta kulla cinikin da kamfaninsa, ya bayyana siffar yadda na’urorin za su kasance, wadanda suka hada da dawakai da mikiyar tambarin Najeriya, wadanda za a tabbatar siffarsu ta fito a jikin na’urorin.
Wannan dan kasuwa ya yi amfani da wannan damar domin ya tallata kwarewar kamfaninsa a harkar hada-hadar kasuwanci, ba tare da la’akari da tayar da jijiyar wuyan da kalamansa za su haifar a kasar nan  da ke fafutikar yaki da cin hanci da rashawa, da kokarin gyaran tsarin ilimi, tare da dimbin matsalolin da suka zame wa kasar manyan kalubale. Baa bin mamaki ba ne ganin cewa ’yan Najeriya sun soki lamirin wannan almubazzaranci da ya bayyana karara. Sai dai Minista Yada Labarai, Mista Labaran Maku, ya yi hanzarin karyata kalaman Mista Ali, sannan ya karyata cewa akwai hannun Gwamnati a cikin wannan lamari.
Mista Maku ya bayyana cewa Fadar Shugaban ba ta da hannu a cikin lamarin. Daga bisani kamfanin ya fito da sanarwar janye kalaman, inda ya bayyana cewa ba ruwaito kalaman Mista Ali daidai ba. Domin bayani kawai ya yi kan yadda za a zayyana tambarin Najeriya a kan na’urorin. Sai kawai cikin hanzari kamfanin ya bayyana cewa wannan odar na’urorin iPhone wani dan Najeriya ne ya bayar da ita, kuma baya son a ambaci sunansa.
Gwamnati ce kadai ke da ikon amfani da tambarin Najeriya bisa tanadin doka. Wannan sanannar gaskiya ce, don haka masu aikata ayyukan zamba cikin aminci ke samun nasara idan suka yi amfani da tambarin Najeriya, a irin almundahanar da suke shiryawa, ta hanyar yaudara wajen gabatar da takardun hukuma. Idan har mutane masu zaman kansu za su iya sanya a kera musu kayayyaki ko na’urori masu dauke da tambarin Najeriya ba tare da izinin gwamnati ba, don haka wannan mummunan laifi ne da ya kamata a udanar da bincike a kai. Lallai gwamnati ta sa a gano kowane mutum ne ke da hannu  ta hanyar la’akari da damuwar al’umma kan wannana bin kunya, tamkar dai yadda Mista Maiku ke nuni da hakan. Akwai bukatar ’yan sanda su binciki wannan cinikin kaya, a kuma gano hakiknain manufar yin hakan. Nuna halin ko in kula daga hukumomi ke yi, zai sanya  masu shakku (gaskiyar gwamnati) sun tabbatar da cewa akwai ma sauran bayanai a kan al’amari fiye ma da abin da aka ji, kafin a gani a zahiri.
Najeriya na dimbin hamshakan masu dukiya, wadanda suka himatu wajen tallafa wa marasa galihu, kuma babu daya daga cikinsu da zai karyata cewa yana kashe kudi ko wane boyayyen mutum ne ya yi wannan ciniki? Ko wane ne ya yi shirin sarayar da Naira miliyan 680 don murnar bikin zagayowar ’yancin Najeriya, sai ya fito ya yi alfahari da gudunmuwarsa, ba tare day a boye gaskiyar lamari ba.
Damuwar masu mu’amala da shafukan sadarwar intanet ta tabata, duk da cewa babu hujja a kan haka, tunda a irin wannan lokaci, a na zargin gwamnati na da hannu wajen odar kayayyakin. Hukumomin gwamnati, musamman wadanda ke samar da kudi tsagwagwa, sun saba sayen kyaututtukan alfarma masu tsada, don bai wa bakin kasashen waje. Hakki ya rataya akan hukumomi su shawo kan wannan al’amari, ta hanyar bayyana mutumin da ke hankoron samar wa kasar nan wadannan kayayyaki.