✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adashen kurma

Kurma ne ya shiga adashe, aka ba shi daukar fari. Ko da matarsa ta gan shi da kudi masu yawa sai ta tambaye shi cewa…

Kurma ne ya shiga adashe, aka ba shi daukar fari. Ko da matarsa ta gan shi da kudi masu yawa sai ta tambaye shi cewa wa ya ba shi. Ya ce mata adashe aka ba shi, sai ta ce masa: “Adashe fa!” Ya amsa mata, sai ta nuna masa cewa ya kiyayi kansa adashe rikice ne. Kurma da jin haka sai ya ce to ya fita daga adashin. Ranar zubi aka ce masa ya kawo zubi sai ya ce: “A’a, ni na fita, domin matata ta ce adashe rikici ne.” Aka ce ya kawo kudin da aka ba shi sai ya ce: “Na kashe su.”
Daga Aminu M. Mai’aduwa, 07038243900