✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adamawa kueens za su samu diyya

Gwamnatin Jihar Adamawa ta yi alkawarin biyan diyya ga  ’yan kwallon mata na Jihar Adamawa da ake kira Adamawa kueens bayan fashi da makamin da…

Gwamnatin Jihar Adamawa ta yi alkawarin biyan diyya ga  ’yan kwallon mata na Jihar Adamawa da ake kira Adamawa kueens bayan fashi da makamin da aka yi musu a kan hanyarsu ta zuwa Benin a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekara.

’Yan fashin sun tare ’yan kwallon da jami’ansu ne a kan hanyarsu ta zuwa Benin da ke Jihar Edo don halartar gasar rukuni-rukuni na ’yan kwallon kafa na mata.

A yayin fashin, rahotanni sun ce ’yan kwallon da jami’ansu sun yi asarar kayayyakin miliyoyin Naira da suka hada da kudi da wayoyin hannu da suturu da sauransu.

Emmanuel Zira, Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Adamawa kueens ya ce gwamnatin Jihar ta kammala shirye-shiryen biyansu diyya game da asarar da suka yi bayan ’yan fashi da makami sun yi musu kwanton bauna a hanyarsu ta zuwa Benin da ke Jihar Edo a kwanakin baya.

Sai dai shugaban ya bukaci gwamnatin jihar da ta rika samar musu kudin zirga-zirga a kan lokaci a duk lokacin da za su tafi wasa.

“Ina shawartar Ma’aikatar kula da wasanni ta jihar da ta rika sakar mana kudin tafiye-tafiye zuwa wasanmu na waje a kan lokaci, don gudun kada irin haka ta sake faruwa. Da muna samun kudinmu a kan kari, ba za mu rika tafiyar dare mai tattare da hatsari ba”.

Wani jami’i da ke aiki a ma’aikatar kula da wasanni ta jihar wanda bai so a ambaci sunansa ba ya ce tuni ma’aikatarsa ta tattara bayanan kayayyakin da ’yan kwallon suka yi asarara a lokacin fashin don a biya su diyya.

Ya ce daga yanzu gwamnati ta yanke shawarar sakar wa ’yan kwallon kudin tafiye-tafiye a kan lokaci don kare su daga sake fadawa komar ’yan fashi a nan gaba.

A tattaunawar da aka yi da wasu daga cikin ’yan kwallon da kuma jami’ansu, sun nuna farin cikinsu ne game da wannan mataki da gwamnatin jihar ta dauka na biyansu diyya, kuma hakan zai karfafa musu gwiwar ci gaba da nuna kwazo a gasar.