’Yar takarar Gwamnan Jihar Adamawa a jam’iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani, ta karyata zargin cewa ta bayar da cin hancin Naira biliyan biyu domin a ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben.
Ta ce sam zarge-zargen ba su da tushe ballantana makama, kuma ba za ta taba yin hakan ba a matsayinta na wacce ta yi amanna da tsarin Dimokuradiyya.
- An tsinci gawar dan Najeriya mai danin jirgin sama a Netherlands
- INEC ta ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Adamawa
Ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar da daren Talata, jim kadan bayan Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Ahmadu Fintiri na PDP a matsayin wanda ya lashe kujerar Gwamnan Jihar a karo na biyu.
A cewar Binani, “An jawo hankalina a kan wasu zarge-zarge marasa tushe da aka ce wani jami’in DSS da aka titsiye ya yi cewa na bayar da Naira biliyan biyu ga wasu jami’an INEC da ba a bayyana sunansu ba. Ban taba yin haka ba, kuma ba zan taba ba.
“An yi wadannan kalaman ne lokacin da jami’an tsaron Fadar Gwamnatin Adamawa da wasu ’yan daba suke titsiye shi.
“Abin da ya faru a Adamawa wani kokari ne da aka yi na kwacewa mutanen Jihar abin da suka zaba. An kwace ikon komai ta haramtacciyar hanya daga hannun Kwamishinan Zaben Jihar, ta hanyar turo wasu manyan Kwamishinonin hukumar biyu daga Abuja.
“Mun damu matuka da yadda wadanccan Kwamishinonin suka kai wa Gwamna Fintiri ziyara bayan isarsu Jihar, inda kuma aka bayyana cewa shi ya lashe zaben a dai wannan ranar, ba kunya ba tsoron Allah.
“Ina kira ga duk masu rajin kare Dimokuradiyya ba a iya Adamawa kawai ba, har ma da sauran sassan Najeriya da su yi duba na tsanaki a kan wadannan abubuwan,” in ji ta.
Daga nan sai ta gode wa magoya bayanta kan yadda suka jajirce wajen mara mata baya duk da yadda aka yi kokarin danne su.