✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adam Zango ya yi nasiha kan abokantaka

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Adam Abdullahi Zango ya yi nasiha mai kama jiki kan abokatanka, inda ya bayyana cewa abokai sun kasu kashi hudu ne.…

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Adam Abdullahi Zango ya yi nasiha mai kama jiki kan abokatanka, inda ya bayyana cewa abokai sun kasu kashi hudu ne.

Jarumin ya bayyana cewa hakika kowanne mutum da Allah Ya ba daukaka ko daraja a wani fanni na rayuwa dole sai ya samu masoya, kamar yadda kuma zai iya samun makiya da mahassada daban-daban.

Zango ya bayyana hakan ne cikin wata nasiha da ya fitar a shafinsa na Instagram a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya ce, akwai wanda yake da’awar cewa shi masoyinka ne, amma ba zai tashi kusantarka ko nuna maka soyayya ba, sai lokacin da ya ga wata nasara ta samu gare ka. 

“Amma idan kishiyar nasara (wato asara) ta samu, ba za ka gan shi ba. Dama ni’imar ce ta kawo shi, to wannan ba abokin kirki ba ne, ba masoyin gaske ba ne. Ka yi hankali da shi,” inji Zango.

Ya ce, akwai wanda yana nan tare da kai ko da yaushe, amma duk abin da ka sa a gaba sai ya taya ka ku yi, ba ya yi maka musu, ko gyara a cikin lamarinka ko da ya gan ka a kan kuskure haka zai taya ka ku yi, to wannan masoyi ne amma yana da rauni a cikin soyayyarsa.

“Akwai wanda yana tare da kai ko yaushe amma idan ya ga abin alkhairi tare da kai sai ya binne labarin. Idan kuma ya ga mummunan abu tare da kai sai ya watsa wa duniya. Ta wajensa ake samun miyagun labarai game da kai, to wannan makiri ne. Ka nuisance shi tun kafin ya yi maka illa. Idan kuma ba zai yiwu ka nisance shi ba, to lallai ne ka rika boye masa sirrinka,” inji Zango.

Ya kuma kara da cewa, akwai masoyin da ko yaushe yana tare da kai a zuciyarsa ko kuma a fili, duk lokacin da ya ganka a kan alkhairi sai ya taimake ka ku yi. Idan kuma ya gan ka a kan kuskure sai ya gyara maka ko da ranka ba ya so, to wannan shi ne masoyi na gaskiya, a rike shi da kyau domin irinsa suna da wahalar samu.

Ya ce, “Hakika Allah yana cewa: “Masoya a wannan ranar (wato Alkiyama) sashensu abokan gaba ne ga sashe. Wato a ranar Alkiyamah abokai za su zamanto masu kin gamuwa da abokansu, saboda tsoron ko za su yi jayayya da su a gaban Allah.”

Ya ce, amma wadanda suka gina abotarsu bisa gaskiya da rikon amanar juna da tsoron Allah, su ne za su rabauta, za su zama sanadiyyar samun rahama ga junansu, kamar yadda hadisai da dama suka tabbatar. 

“Ya Allah ka hada mu da mutanen kirki masu kaunarka, kuma wadanda soyayyarmu da su za ta amfane mu a wajenka. Ka raba mu da miyagun abokai na fili da na boye. Ka kiyaye mu daga sharrinsu da makircinsu,” inji Zango.