Gwanayen ninƙaya a ranar Alhamis sun sake gano ƙarin wasu gawarwaki takwas daga kogin da wani kwale-kwale da yake ɗauke da fasinjoji ‘yan Maulidi ya kife a yankin Gbajibo da ke Karamar Hukumar Mokwa a Jihar Neja.
Gano gawarwakin ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa 24, kamar yadda Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa NEMA ta bayyana.
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda biyu a Anambra
- Najeriya ta soke harajin VAT a kan iskar gas da man dizel
Aminiya ta ruwaito yadda kwale-kwalen da ya taso daga garin Mundi ya kife da fasinjoji kusan mutum 300 a ranar Talata.
Darakta Janar na Hukumar NEMA, Alhaji Abdullahi Baba Arah, ya ce tun farko an gano gawarwakin mutanen 16 da suka haɗa da mata 2 da maza 14 a ranar Laraba kuma aka binne su a unguwar Gbajibo.
Arah ya ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki na cikin gida don gano waɗanda haɗarin ya rutsa da su.