✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Adadin masu kamuwa da Coronavirus na kara raguwa a Najeriya

Adadin sabbin masu kamuwa da  COVID-19 ya kara raguwa a kwana na biyu a jere a Najeriya. Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta…

Adadin sabbin masu kamuwa da  COVID-19 ya kara raguwa a kwana na biyu a jere a Najeriya.

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa ranar Lahadi an samu mutum 170 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa, “Zuwa karfe 12.00 na daren 3 ga watan Mayu, mutum 2,558 ne aka tabbatar da sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Daga cikin wadannan mutum 170 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan dai, 39 a jihar Legas suke, sai 29 a Kano, 24 a Ogun, 18 a Bauchi, 15 a Kaduna, 12 a Yankin Babban Birnin Tarayya da Sakkwato, takwas a Katsina, bakwai a Borno, uku a Nasarawa, biyu a Adamawa, sai jihar Oyo da ke da karin mutum daya.

Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 400 bayan sun samu sauki, yayin da mutum 87 suka riga mu gidan gaskiya.

A karo na biyu da hukumar NCDC ta yi sanarwar, alkaluma sun nuna cewa ana samun raguwar sabbin masu kamuwa da cutar a Najeriya.