Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta bayyana marigayi Sarkin Kungiyar Ibo (Ohanaeze Ndigbo), Farfesa George Obiozor a matsayin mutum mai sasanta tsakani wanda za a yi rashin shugabancinsa.
Cikin sanarwar da ta fitar ranar Lahadi ta hannun wani jagoranta, Cif Audu Ogbeh, kungiyar ta ce rasuwar marigayin za ta yi tasiri kan kokarin da kasa ke yi na tabbatar da zaman lafiya da lumana a tsakanin al’ummomi kasar.
- Tinubu da Atiku sun yi wa Obasanjo raddi kan goyon bayan Obi
- Mutum 7 sun mutu, 16 sun jikkata a hatsari ranar Sabuwar Shekara
Ogbeh ya ce, “ACF ta kadu da samun labarin mutuwar Farfesa Obiozor George Achulike, Shugaban Kungiyar Ohanaeze Ndigbo, wanda Gwamnan Jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya sanar.
“Hakika wannan babban rashi ne musamman a wannan lokaci da ke da bukatar salon shugabanci abin koyi irin nasa.”
ACF ta ce tarihi ba zai mance da gudunmawar da marigayin ya bayar ba ga ci gaban al’umma.