Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce haramcin da ta sanya kan kafa shingayen binciken ababen hawa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna na nan tana aiki.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya jaddada umarnin a sakon da ya fitar a ranar Asabar, sakamakon korafe-korafen jama’a game da samuwar shingayen binciken a kan hanyar.
- An gano yarinyar da fasto ya sace bayan shekara 7
- ’Yan sanda sun kashe ’yan fashin mota lahira
- Gwamnati da ‘yan tawayen Sudan sun amince su tsagaita wuta
“Tun a bara Majalisar Tsaron Jihar Kaduna ta sanar da jama’ar jihar cewa ta haramta kafa shingayen binciken ababen hawa a hanyar tafiya da dawowa tsakanin Kaduna zuwa Abuja da sauran hanyoyi.
“Duk wanda aka kama ya kafa shingen bincike a kan wadannan hanyoyi ya aikata haramtaccen abu kuma da hakan za a hukunta shi.
“Don haka ake umartar dukkannin masu bin hanyar da kada su yi biyayya ga masu kafa shingayen binciken.
“Wannan sanarwar na shawartar jama’a da su kai karar duk wanda ya saba umarnin nan ga cibiyar tsaro ta kan wadannan lambobin kar-ta-kwana: 09034000060, 08170189999’’, inji kwamishinan.
A watan Satumban 2019 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta soke binciken ababen hawa a kan hanyar, wadda ta yi kaurin suna wajen ayyukan masu garkuwa da mutane da fashi da makami.
Matsalar garkuwa da mutane a babbar hanyar ta yi sanadiyyar salwantar daruruwan rayuka ciki har da na sarakuna, ‘yan kasuwa kasuwa da ‘yan siyasa da da jami’an tsaro da dalibai baya ga asarar dimbin dukiyoyi da ake bayarwa a matsayin kudin fansa.
Halin lalacewar hanyar da matsalar tsaro a kanta sun sa dubban masu bi ta hanyar sun gwammace su bi jirgin kasa domin tsira da rayuwarsu.
Matsalar garkuwa da mutane a jihar Kaduna ta fi yin kamari a hanyar wadda ita ce mashigin birnin tarayya zuwa Kudancin Najeriya daga bangaren da kuma hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari wadda ita ma take a matsayin babbar hanyar da ta hada yankin jihar da babbar hanyar da ke kaiwa zuwa Kudancin Najeriya.