Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya ce a bayyane Majalisar za ta gudanar da aikin tantance Abdulrasheed Bawa, wanda Shugaba Buhari ke son nadawa Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC).
Ahmad Lawan ya bayyana haka ne bayan karanta wasikar neman amincewar Majalisar da Buhari ya aike mata a safiyar Talata.
- Buhari ya nada dan shekara 40 a matsayin sabon Shugaban Hukumar EFCC
- Yadda ’yan Arewa ke kaura daga Ibadan bayan rikicin Sasa
- Rundunar Sojan Sama ta sanar da bude shafin daukar aiki
- Wata sabuwa: Cutar Ebola na sake barazana ga Najeriya
“Tantance Shugaban EFCC da aka ayyana zai gudana ne a zaman zauren Majalisa da aka saba a nan,” inji shi bayan karanta takardar da nadin Abdulrasheed Bawa da Buhari ya aika wa Majalisar.
Bawa mai shekara 40 daya ne daga cikin kananan hafsoshin farko da EFCC ta dauka aiki a 2005.
Yanzu shi ne Shugaban Ofishin Hukumar da ke Legas, wanda shi ne mafi muhimmanci bayan Hedikwatarta da ke Abuja.
Idan aka amince da nadin nasa, zai gaji Mukaddashin Shugaban Hukumar, Mohammed Umar da ke rikon mukamin tun watan Yulin 2020 bayan an dakatar da Ibrahim Magu bisa zargin almundahana.
EFCC ta yi kusan shekara hudu ba tare da Shugaba cikakken iko ba tun bayan da Majalisa ta takwas ta ki amincewa da nadin Magu bisa zargin almundahana.
Bawa na da shaidar Digirin Farko a fannin Tsimi da Tanadi daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo, da ke Sakkwato inda kuma ya Digirinsa na biyu a fannin Diflomasiyya.