Mun iske kanmu da nau’o’in man shafawa da mata da dama ba su san da me ake hada su ba. Su dai daga ganin ya yi kyau sai a ce zai yi wa fata kyau.
Yawan shafa irin wadannan mai na haifar da kuraje wadanda ba su barin fuska. Kuma ko da sun bar fuska sai a ga tabon na nan ba ya bata.
- Mutum 17 sun mutu a wajen sharholiya a Afirka ta Kudu
- Labaran ma’aurata: Na rufa masa asiri sai na tarar da farin ciki
Don haka a yau na kawo muku abubuwan kwalliya shida wadanda ko a gida za a iya hada su don samun fata mai laushi kuma mara kuraje.
- Man zaitun: Yana dauke da sinadaran rage maiko a fuska. Don haka yana da kyau idan za a sake yin kwalliya a samu auduga a tsoma a man zaitun a rika goge fuskar da ita kafin a sake yin watakwalliyar. Yin haka na hana fesowar kuraje a fuska.
- Kwakwa: Sai a ga mace fara kyakkyawa, amma da za a taba hannunta sai a ji kamar tana faskare ko surfe tsabagen tauri. Idan ana da irin wannan matsalar, sai a samu kwakwa a kankare bayanta sannan a markada da ruwa kadan a tace a sa a firiji. Idan ta yi sanyi sosai sai a rika shafawa a tafin hannu tana sa fatar hannu laushi.
- Zuma da sukari: Idan mutum na fama da fata mai yawan saba musamman fatar fuska, sai a hada zuma da sukari a wuri guda, sai a shafa a fuska na tsawon minti 30 kafin a murza a fuska. Yin hakan na cire fatar da ta mace a fuska don ba sabuwar fata waje. Idan an gama sai a wanke da ruwan dumi. Abubuwan kwalliya shida da fata ke bukata
- Kindirmo: Yana sa fatar fuska laushi da sulbi. A samu kindirmo a shafa a fuska na tsawon minti 30 a kullum kafin a kwanta barci. Yin haka na kashe kowace irin kwayar cutar da take fesowa a fuska ko a fata.
- Kwai: A samu ruwan kwai a cire kwaiduwar a rika bugawa har sai ya yi kumfa. A shafa a gashin kai na tsawon awa daya ko rabin awa sannan a wanke da man wanke gashi. Yin haka na cire daudar da ke cikin gashi da kuma hana gashi karyewa.
- Fiya: Shi ma yana gyara gashi sosai. A kwaba shi ya yi laushi sannan a shafa a fatar kai don hana fesowar amosanin ka. A bari a fatar kai na tsawon minti 30 kafin a wanke da ruwan dumi.