✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da zan bai wa muhimmanci idan na zama Shugaban Kasa – Hashim

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar Peoples Party, Cif Gbenga Olawepo-Hashim ya soki tsare-tsaren gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya sha…

Dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar Peoples Party, Cif Gbenga Olawepo-Hashim ya soki tsare-tsaren gwamnati mai ci ta Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya sha alwashin kawo sauyi idan ya samu nasara a zaben da ke tafe

Cif Olawepo-Hashim wanda ya bayyana haka a yayin kaddamar da yakin neman zabensa a ranar Asabar da ta gataba a Abuja, ya ce matsalar rashin aikin yi ga matasa, zai yi wuya a magance ta a tsarin da ake tafiya a kai a yanzu.

Ya ce “Abu na farko da zan fara yi idan na samu nasara shi ne ragw karfin Gwamnatin Tarayya tare da kara karfi ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ta yadda za su iya samar da dukiyarsu ta kashin kansu don gudanar da ayyuka ba tare da dogaro ga kason tarayya da su ke yi ba a yanzu. Kuma zan goyi bayan tsarin samar da ’yan sandan jihohi ta yadda za su rika gudanar da ayyukansu hannu-da-hannu da ’yan sandan tarayya, sannan in kirkiro rundunar tsaro ta kasa (National Guard) da za ta cike gibin gudanar da ayyuka da ya dara na ’yan sanda, amma bai kai na soja ba, don rage dogaro a kan sojoji.”

“Zan samar da yanayin da kowane dan Najeriya zai yi alfahari da kasarsa a duk inda yake a duniya sannan in inganta makarantunmu a dukan matakai,” inj shi.

Dan dan takarar ya ce zai kasance babban kwamandan tsaro ga kasa baki daya, maimakon kasancewa na wani sashi ko addini ko kabila.

Taron wanda ya samu halartar wadansu ’yan siyasa kamar su Alhaji AbdulJalil Tafawa Balewa da Misis Funke Awolowo da Mista Olisa Agbakoba da sauransu, ya gudana ne a Dandalin Fareti na Abuja.

Kuma taron ya samu halartar dimbin matasa da mata wadanda jam’yyar ta ce za ta kyautata rayuwarsu ta hanyan ba su jarin yin sana’a ko noma bayan an ba su horo.

Sai dai har zuwa lokacinkare taron wanda aka bayyana a matsayin babban daraktan kamfe na dan takarar, tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’abba bai bayyana a wurin ba, kuma ba wani bayani a kan dalilin rashin zuwarsa.