✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abubuwan da ya kamata ku sani a kan ranar Hausa ta Duniya

Ana amfani da yaren a kasashe 32 daga cikin kasashen Afirka 54

Bincike ya nuna cewa Yaren Hausa shi ne na 11 a jerin yarukan da aka fi amfani da su a duniya, kuma na farko a Afirka ta Yamma.

Yaren Hausa dai na da masu amfani da shi sama da mutum miliyan 150 da suka warwatsu a kasashe sama da 30, kuma shi yake biye wa Faransanci a yawan masu amfani da shi a duniya.

Ana amfani da yaren a kasashe 32 daga cikin kasashen Afirka 54 bayan sun yi hijira zuwa can saboda dalilai daban-daban.

Hatta a kasar Sudan, bincike ya nuna akwai Hausawa kimanin miliyan 10 ’yan asalin kasar.

An dai fara gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya ne a shekarar 2015 a kafafen sada zumunta na zamani.

A lokacin dai, wani ma’aikacin Sashen Hausa na BBC, Abdulbaki Jari ne da wasu abokansa suka fara bikin ranar domin samar wa da masu amfani da yaren damar tattauna abubuwan da ke ci wa yaren tuwo a kwarya.

Daga bisani a shekarar 2018, an fara gudanar da bukukuwa na zahiri a Gidan Dan Hausa da ke Jihar Kano da ma wasu sassa na duniya, ciki har da a kasar Ghana.

Wadanda suka kirkiro bikin sun ce sun yi hakan ne da nufin tuna wa al’ummar Hausawa muhimmancin yarensu da kuma tara su a waje daya domin tattauna yadda za a inganta shi.

Ya zuwa shekarar 2020, an gudanar da bikin Ranar Hausa a kasashe sama da 25 na fadin duniya, ciki har da Faransa da Saudiyya.

Masana dai sun ce Hausa na daya daga cikin yarukan da suka fi saurin yaduwa a duniya, inda hatta manyan kamfanonin sadarwa irinsu Facebook da Google da IOS sai da suka saka shi a jerin yarukan da suke amfani da su.

Ko a ’yan shekarun nan ma, Hukumar Lafiya ta Duniya ta saka Hausa a jerin yarukan da take amfani da su wajen yaki da annobar COVID-19.

Kazalika, a shekarar 2020 ma, kasar Saudiyya ta saka Hausa a jerin yaruka 10 da take amfani da su wajen fassara hudubar ranar Arfa, taron addini mafi girma a duniya.