Duk shekara ana samun ci-gaba da bunkasa a harkokin adabi da marubuta. Yayin da sababbi da tsofaffin marubuta ke ta kokari da ba da gudunmawa don ganin sun kawo sauye-sauyen da za su farfado da harkar talifin littattafan Hausa da kasuwancinsa a kasuwanni da shagunanan littattafai na zahiri da na yanar gizo.
Manufar wannan rubutu shi ne ya yi bita kan wasu muhimman abubuwa da suka faru cikin wannan shekara mai karewa. Za mu fara bitar ne daga Jihar Jigawa, inda a ranar 13 ga watan Fabarairu kungiyar Marubutan Jihar Jigawa (JISWA) ta gudanar da taron hadin kai da wayar da kai tsakanin marubuta da mawaka na jihar, wanda ya gudana a karamar Hukumar Hadejia, a dakin taro na UBJ Hall da ke cikin garin Hadejia.
- Mutum 17 sun rasu wajen rububin kudi a unguwar Hausawan Kalaba
- Waiwayen abubuwan da suka faru a yajin aikin ASUU na 2022
A Jihar Kano babbar Cibiyar Dandazon Marubuta Littattafan Hausa, Manazarta da Masu Fasahohi da kirkirar Wakoki ta Arewa, har wa yau kuma tsohuwar Cbiyar Kasuwanci Littattafan Hausa da aka fi sani da Adabin Kasuwar Kano ta shirya taron liyafa don taya murna ga daya daga cikin mambobinta, fitaccen marubuci kuma mawaki Aminu Ladan Abubakar da aka fi sani da ALAN Waka, wanda Masarautar Gobir ta yi wa nadin sarautar Sarkin diyan Gobir.
Bikin wanda ya gudana a Dandalin Taro na gidan rediyon Premier FM a ranar 14 ga watan Maris, 2022. An baje kolin fasahohi iri-iri na mawaka da raba kyaututtuka ga marubutan da suka samu nasara a gasar gajeren labari da kungiyar marubuta ta HAF ta shirya, don karrama Sarkin diyan Gobir.
A wajen taron ne kuma har wa yau, aka gudanar da yayen rukunin farko na daliban makarantar koyar da dabarun rubutun gajeren labari da fim ta Kwalejin Marubuta Hausa (Hausa Writers College) da wasu jajirtattun marubuta suka kafa.
Makarantar ta yaye matasan marubuta 38 wadanda suka samu horo ta hanyar kwasa-kwasan da aka rika koyar da su ta manhajar WhatsApp Wani fitaccen marubuci, Jibrin Adamu Rano da aka fi sani da Barista ya fitar da wata sanarwa a shafinsa na Facebook a ranar 8 ga watan Mayu, inda ya nemi marubutan kafar sadarwa da ba su samu damar buga littafinsu ko sau daya ba, su aika da neman shiga cikin wadanda za su samu garabasar buga musu littafinsu kyauta da zai dauki nauyi ga marubuta 20 da suka cika wasu sharuda.
A ranar 5 ga watan Yuni, kimanin wata daya da fitar da sanarwa, kashin farko na littattafan da aka yi alkawarin bugawa kyauta sun fara fita. Sai dai an fara ne da fitar da littattafai guda uku, wadanda suka hada da ‘Yar Gantali na Raƙayya Ibrahim Lawal da Baƙar Fura na Fatima Sanusi Rabi’u da kuma Lauje Cikin Naɗi wanda Aminu Lawal Darazo da aka fi sani da Elder ya rubuta.
A ranar 31 ga watan Yuli, Gamayyar kungiyoyin Marubutan Jihar Kano (GAMJIK) ta gudanar da taron mika kyaututtuka ga kungiyoyin marubuta 32 da suka shiga Gasar Muhawara tsakanin kungiyoyin marubuta, wanda aka gabatar ta yanar gizo a manhajar Facebook da kuma kaddamar da littafin muhawarorin da aka gabatar, wanda aka hada su waje guda cikin littafi mai suna ‘Kan Ɗaki Sai Gayya!’ Sakamakon gasar ya nuna cewa, kungiyar Kainuwa Writers Association ce ta yi nasarar lashe gasar a matsayin ta daya, sai kungiyar Zamani Writers Association ta zo ta biyu, yayin da kungiyar Gamayyar Marubutan Nijar ta yi nasarar zuwa mataki na uku.
Kungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Jigawa (JISWA) ta gudanar da taron baje kolin fasaha da zakulo fasihan marubuta na bangarori daban-daban da karrama wasu jajirtattun mata.
A taron, kungiyar ta samu albishir na kyautar ofishi a Dutse wanda Shugaban karamar Hukumar Dutse, Alhaji Bala Chamo da Kwamishinan Kula da Albarkatun Ruwa na Jihar Jigawa, Alhaji Ibrahim Hannun Giwa suka bayar.
A ranar 12 ga watan Afrilu, kungiyar Marubutan Jihar Katsina (KMK) ta gudanar da taron hadin kai da farfado da kungiyar wacce ta yi dogon suma, saboda rashin gudanar da harkoki.
Kamar yadda aka saba, a kowace shekara a ranar 23 ga watan Afrilu, ana gudanar da bikin ranar Littafi da Kare Hakkin Mallaka ta Duniya, inda a bana kungiyoyin marubuta dabandaban suka gudanar da taro na musamman don raya wannan muhimmiyar rana, kamar yadda kungiyar Marubutan Hausa ta Jos Writers Club a Jihar Filato ta gudanar.
Kungiyar marubuta ta Jarumai Writers Association ta gudanar da bikin ba da kyaututtuka da karramawa ga wadanda suka shiga gasar rubutun gajeren labari kan jigon yaki da tabarbarewar tsaro, inda aka fitar da gwaraza mutum 4 da suka taka rawar gani cikin marubuta fiye da hamsin da suka shiga gasar.
A taron da aka gudanar a dakin Karatu na Murtala Mohammed da ke Kano, an karfafa gwiwar marubuta kan yin rubutu mai inganci da bin ka’idojin rubutun Hausa. Wannan taro ya gudana ne a ranar 3 ga watan Yuli.
A wani bangare na kara hada kan marubuta da masu sha’awar rubuce-rubuce a harshen Hausa a Jihar Jigawa, shugabannin kungiyar Marubutan Jihar Jigawa (JISWA) sun kira wani taro a Babban dakin Karatu na garin Dutse, a ranar 31 ga watan Yuli, inda aka tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi bunkasa harkar adabi a Jigawa.
Marubuta daga sassan Najeriya daban-daban sun hallara a birnin Katsinan Dikko don halartar taron shekarashekara na Marubutan Arewa, wanda aka saba shiryawa da nufin tattauna sababbin hanyoyin inganta harshen Hausa da al’adun Hausawa.
Taron ya gudana ne a ranakun 9 zuwa 12 ga watan Satumba, 2022, karkashin taken “Rubutun adabi da inganta harsunan gado a matsayin hanyoyin magance matsalolin tsaro a arewacin Najeriya.”
Fitattun malaman jami’o’i da manazarta harshen Hausa daga jami’o’i daban-daban na Najeriya ne suka halarci taron da gabatar da makaloli kan sakamakon binciken da aka gudanar, tare da gabatar da raye-rayen gargajiya da rubutattun wakoki.
Daga ranakun 2 zuwa 5 ga watan Nuwamba, kungiyar Marubuta ta kasa wato Association of Nigerian Authors (ANA) reshen Jihar Kano ta gudanar da taron Makon Marubuta da aka yi wa taken “Rubutu: Ginshikin Yayata Al’adun Hausawa Ga Al’ummar Duniya,” wanda aka gabatar a dakin karatu na Murtala Mohammed da ke Kano. A ranar 3 ga watan Nuwamba, Sashin Hausa na BBC ya gudanar da bikin karrama gwarazan Gasar Hikayata ta 2022 a wani kayataccen taron da aka gudanar a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda a karon farko wata marubuciya daga Jamhuriyar Nijar Amira Souley ta zama gwarzuwa da labarinta na ‘Garar Biki’, sai Hassana Labaran dan Larabawa da ta zama ta biyu da labarinta ‘Haihuwar Guzuma’, yayin da malama Maryam Muhammad Sani ta zama ta uku da labarinta mai suna ‘Al’ummata’.
Kashi na biyu na littattafan da fitaccen marubucin nan, Jibrin Adamu Rano da aka fi sani da Barista ya yi alkawarin buga wa marubutan adabi na kafofin sadarwa sun fita.
A wannan karon littattafai 5 ne suka fita wadanda suka hada da ‘Duhun Dare’ na Rakayya Ibrahim da ‘Zubar Hawaye’ na Hadiza D. Auta da ‘Gawa Da Rai’ na Yusuf Yahaya Gumel da ‘kayar Ajali’ na Maryam Abdul’Aziz da ‘Aikin Baban Giwa’ na Binyamin Zakari Hamisu. Littattafan da aka yi ta zumuɗin fitar su tun daga ranar da bangon su ya fara fita a yanar gizo a ranar 22 ga watan Oktoba.
Sakamakon abin farin cikin da ya faru a Gasar Hikayata ta BBC Hausa, inda biyu daga cikin mata ukun da suka yi nasara a gasar ’yan Jihar Kano ne, ya sa Gamayyar kungiyoyin Marubutan Jihar Kano ta GAMJIK ta shirya wani gagarumin taron liyafa don taya su murna da kuma karrama su, a ranar 20 ga watan Nuwamba. Taron ya gudana ne a ɗaƙin taro na American Space da ke Ɗakin Karatu na Murtala Muhammad a Kano, inda manyan masu faɗa a ji a harkar rubutun adabi a Jihar Kano irin su Ado Ahmad Gidan Dabino MON tsohon shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen Jihar Kano ANA suka halarta. Daga 25 zuwa 27 ga watan Nuwamba, marubuta da masu fasahar ƙirƙira a Jihar Borno, sun gudanar da bikin baje kolin littattafai da fasahohi na farko a jihar, wanda aka yi wa lakbi da BOBAFEST, wato Borno Books and Arts Festibal. A yayin taron marubuta na Hausa da Ingilishi daga ciki da wajen jihar suka baje kolin basirarsu a fannoni daban -daban na adabi, da suka haɗa da rubutattun waƙoƙi da waƙoƙin baka da gajerun labarai na littafi da na bidiyo da kuma tattaunawa tsakanin malamai da manazarta game da batutuwan da suka shafi ƙalubalen tsaro da zamantakewa a tsakanin al’ummar Jihar Borno.
A ranar 30 ga watan Nuwamba ne aka gudanar da babban taron miƙa shaidar samun nasara a gasar gajerun labarai da Cibiyar Nazari da Bincike ta Aliyu Mohammed da aka fi sani da Gusau Institute ta gabatar a garin Zariya na Jihar Kaduna, inda aka sanar da cewa, Malama Bilkisu Garkuwa ita ce ta zama ta ɗaya da labarinta mai suna ‘Ƙaddarar Rayuwa’, yayin da Malama Hajara Ahmad OumNass ta samu zama ta biyu da labarin ta mai taken ‘danyen Kasko,’ sai na uku wanda shi ne namiji a cikinsu wato Muttaka A. Hassan da ya samu nasara da labarinsa mai suna ‘daukar Jinka’.
Daga ranakun 1 zuwa 5 ga watan Disamba aka gudanar da Bikin Baje-kolin Littattafai da Fasahohin Hausawa mai lakabi da HIBAF 2022 wanda aka saba gabatarwa duk shekara a Jihar Kaduna.
An gabatar da bayanai da nazarce- nazarcen masana harshen Hausa da al’adun Hausawa, inda aka zazzage ilimi da sakamakon bincike a kan ci-gaban rayuwar Malam Bahaushe da bunkasar adabin Hausa da raye-rayen al’adun gargajiya da karatun littattafan Hausa daga marubuta maza da mata.
Taron ya kuma samu mahalartar marubuta da masana da manazarta da mawaka daga ciki da wajen Najeriya. Ga waɗanda ba su samu damar halartar taron HIBAF na Kaduna ba, an gudanar da wani makamancinsa a Birnin Kano a ranar 16 ga Disamba, inda hadin gwiwar wasu kungiyoyin raya al’adu na Open Arts da Legacy of Tradition.
Cibiyar Nazarin Harsunan Najeriya da Fassara da Hikimomin Al’umma ta Jami’ar Bayero da ke Kano ce ta gabatar da taron tunawa da Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, a ranar 22 da watan Disamba, karkashin taken “Halaye da dabi’u A Cikin Tatsuniyoyin Hausawa”.
Fitattun shaihunan malamai da tsofaffin abokan marigayin ne suka samu halartar wannan taro wanda shi ne irin sa na farko, domin yabawa da gudunmawar da tsohon fitaccen marubucin littattafan tatsuniya da ilimantar da ƙananan yara al’adu cikin harshen Hausa ya bayar a lokacin rayuwarsa. kungiyar Marubuta Labaran Adabi ta Madubi da ke Jihar Maradi, sun shirya wata liyafa ta musamman don taya shugabarsu kuma Gwarzuwar Gasar Hikayata ta 2022 Ameerah Souleymane, a ranar 24 ga watan Disamba.
Wannan taro ya samu halartar shugabannin kungiyoyin marubuta adabin Hausa daga Najeriya, karkashin jagorancin shugaban masu shirya finafinai na Jihar Kano, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON.