Da ana yin amfani da wasu abubuwa hudu a Najeriya wato arzikin kasa, mutanen kirki, ilimi da hankali da ba mu shiga irin mawuyacin halin da muke ciki a yanzu ba.
Ministar Kudi ta lokacin Buhari ta ce, fiye da kashi 95 na danyen man Najeriya wasu jami’an gwamnati da sojoji da ’yan sanda ne suke sacewa!
- Gwamnatin sojin Nijar ta janye jakadan kasar a Ivory Coast
- Yanzu-yanzu: DSS ta gurfanar da Emefiele kan sabbin laifuka 20
Har yanzu gwamnati ba ta dauki matakin kamo su da kwato dukiyar da suka sace aka hukunta su ba.
Tsohuwar Ministar Mai ta lokacin Shugaba Jonathan, Dezeini Madueke ana zargin ta gudu da kudin mai da yawansu ya kai a yi kasafin kudin Najeriya na fiye da shekara biyar, ita ma har yanzu ba a dawo da ita, aka kwato dukiyar da ta sace aka hukunta ta ba.
Ga kudin gyaran matatun mai guda biyu, Dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 900, ba a gyara ko daya ba, ina kudin?
Sai dakataccen Gwamnan Babban Banki (CBN), Godwin Emefiele da tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami da ake zargi game da wasu abubuwa a CBN da NNPC da sauran wadanda ake zargi.
Sai kudin wutar lantarki da ake zargin su Olusegun Obasanjo da dannewa kuma ga zargin da ake yi masa kan Library dinsa da gonarsa da sauransu.
Ga rahotanni birjik na Hukumar EFCC a karkashin Malam Nuhu Ribadu da Farida Waziri.
Ga kotun rusassun bankuna (Failed Banks Trabunal) na lokacin Janar Sani Abacha.
Sai zargin wadaka da kudin ajiyar waje da aka yi wa gwamnatin Abdussalami Abubakar da kuma zargin handame Dalar Amurka biliyan 20 a zamanin Shugaba Ebele Jonathan.
Ga kwamitin Pious Okigbo kan CBN ga zargin karkatar da rarar kudin yakin Tekun Fasha Dalar Amurka biliyan 12.2 a zamanin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Sai kuma zargin da ake kira da Abacha Loot. Kusan duk inda ka waiwaya barna ce a bayan barna, duk masuyin dokoki da masu zartarwa da hukumomin shari’a da jami’an tsaron kasa musamman sojoji da ’yan sanda da kwastam babu na dauka.
Don haka ba za a yi maganin halin da ake ciki ba matukar ba a fara yin bincike ana hukunta masu laifi ba wato a koma baya a fara hukunta wadanda ake tuhuma in ana so a gyara kasar nan.
Wajibi ne in ana so a mayar da kasar nan kan turbar kwarai a kwato dukiyar da kowa ya sata, a hukunta su a bainar jama’a.
Babu wata kasa a duniya da shugabanninta suke yi wa satar da ake yi wa Najeriya.
Barayin shugabannin Najeriya sun hada kai sun kirkiro wata hanyar satar tsiyata talakawa da talauta masu dukiya ta halal da sunan tallafin mai wanda babu wani abu mai kama da tallafi a harkar mai, tunda muna da mai a kasar nan da matatun mai guda hudu.
Kuma kullum muna hako har ganga miliyan uku ko fiye inda babu wanda ya san adadin yawan man da ake hakowa a Najeriya saboda sata da kisa.
Har masu yin dokoki da suke biyan kansu albashi fiye da ninki dubu na kananan ma’aikata, yayin da mafiya yawanmu ba su da aiki ko sana’a sai bangar siyasa da roko ko bara da sata.
Masu yin dokoki da masu zartarwa ne kurum suke yi wa kansu tallafin man bayan yin sata karara inda suke sayo kayan miliyan daruruwa su sayar wa kansu a kan miliyan biyar zuwa 10.
Sun bari ana shigo da hodar Iblis da noma wiwi da safarar miyagun kwayoyi masu haukatarwa da aka fara sani tun daga batun Gloria Okon da marigayi Dele Giwa ya so fallasawa.
Ga shi yanzu kusan ana zargin jami’an tsaro ciki har da na NDLEA da zama kamar wakilan masu shigowa da su.
Duk kasar da babu shari’a tana cikin rudu da rudewa, don haka idan mu ’yan Najeriya masu hankali da ilimi da mutunci da yin imani mun damu da wannan bala’i da muke ciki, muna so komai ya daidaita, arzikin kasarmu ya amfane mu, mutanen kirki su amfane mu, ilimi da hankali su yi mana amfani to, lokaci ya yi da za mu fara tanance tsakanin barayi da masu kaya! Ko azzalumai da wadanda ake zalunta.
Duk barayin shugabannin Najeriya da suka sace arzikin kasarmu a bi su a kwato dukiyar da suka sace, kudi da kadara, gida da waje, a hukunta duk masu laifi da na kisa da daurin rai-da-rai, gargwadon satar da suka yi.
Masu mulki hadiman talakawa ne (Public/Civil Servants) su tabbata a kan matsayinsu na masu hidima, mu kuma al’ummar kasa mu tabbata a kan matsayinmu na wadanda shugabanni da masu aikin gwamnati, zababbu da nadaddu da sauran ma’aikatan gwamnati da ake biyansu albashi da alawus daga dukiyarmu, su rika yi mana abin da Allah Ya umarce su da su rika yi mana.
Idan ba su sani ba a sanar da su, idan sun manta a tunatar da su. Bai dace saboda dan abin da za mu rika samu daga kare miyagun shugabanni zababbu da nadaddu ba mu zama wawaye.
Mu daina bari masu mulki suna zama gungun barayin da za su rika hada baki suna fakewa da Boko Haram ko masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da ’yan fashin daji suna tatuke dukiyar kasa ba.
Samuwarsu ta haifar da barayi masu haurawa gidajen mutane suna satar kudi da wayoyin hannu da kisan gilla da fyade, lamarin da ya sa suke neman fin karfin gwamnati mai jami’an tsaro da NAFDAC da NDLEA da sauransu.
Abdulkarim Daiyabu, Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya, Tsohon Shugaban Jam’iyyar AD na Kasa, Tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da Ayyukan Noma ta Jihar Kano. 08023106666, 08060116666.