✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da ke jawo koma baya a gasar Firimiyar Najeriya

A jiya Lahadi ne aka fafata wasanni na 24 a Gasar Firimiyar Najeriya, inda a yanzu kungiyar Platueau United ke saman teburi. Ita dai kungiyar…

A jiya Lahadi ne aka fafata wasanni na 24 a Gasar Firimiyar Najeriya, inda a yanzu kungiyar Platueau United ke saman teburi.

Ita dai kungiyar Platueau United tana kan gaba ne a gasar da maki 46, sai Rivers United ke biye mata da maki 42 sai kuma Lobi Stars na Makurdi ke na uku da maki 40.

Akwai ci gaba da dama da aka samu a gasar, musamman yadda ake ci daga da samun ’yan wasa daga kasashen waje suna zuwa gasar ta Firimiya, wanda ke nuni da cewa akwai abun a zo a gani.

A makon jiya ne wani abun alhini ya faru, inda dan wasan kungiyar Nasarawa United Chieme Martins ya yanke jiki ya fada a wasansu da kungiyar Katsina United.

Wannan lamarin ya jefa gasar da masoya gasar cikin rudu da damuwa, kasancewar mutuwar dan wasan bayan abu ne da wasu suke tunanin bai kai a ce ya kai ga mutuwa ba.

‘Yan wasan sun sha yanke jiki su fada a tsakiyan wasa, amma ba kasafai suke mutuwa saboda kawai sun yanke jiki sun fadi saboda bugun zuciya, amma kasancewar har yanzu an bar Firimiyar Najeriya a baya, sai dan wasan ya mutu.

Wannan ne ya sa Aminiya ta rairayo wasu abubuwa da suke kawo wa gasar tarnaki:

Rashin albashi mai kyau:

A har kullum, burin dan wasan Najeriya da ke buga gasar Firimiyar Najeriya shi ne ya samu ya tsallaka ya bar kasar, ko da kuwa zuwa wata karamar kasa ce da ba ta kai Najeriya arziki ba.

Wannan ke nuna cewa akwai matsalar rashim gamsuwa da abin da suke samu. Sannan duba da cewa za ka dan wasa ya dade tana taka leda, amma kuma babu abin da tsinana.

Ba duka kungiyoyin ba ne ba sa biyan albashin da kyau, domin wasu na biya da kyau kuma a kan lokaci, amma wasu kungiyoyin ba sa biya da kyau, kuma ba sa biya a kan lokaci.

Ya kamata a ce akalla kowace kungiya tana iya biyan albashin ’yan wasanta a kan lokaci, sannan a tabbatar albashin yana da kyau.

Gwamnati za ta iya yin hakan, ta hanyar tursasa kowace kungiya ta bi umarninta, ko kuma a rika hukutna su ta hanyar kwashe musu maki, ko cin tararsu.

Rashin filayen wasa masu inganci:

Har yanzu a wannan fannin an bar Najeriya a baya, kasancewar za ka ana wasa a filin wasa, amma ko dai babu ciyawar, ko kuma ciyawar ta yi girma da yawa da har tana iya tsayar da kwallo.

Wannan ba karamin kalubale ba ne shi ma.

Rashin kwararrun alkalan wasa

Wani abu da ya dade yana ci wa masu kallon gasar Firimiyar Najeriya tuwo a kwarya shi ne rashin kwararrun alkalan wasa ke bata wasanni da dama.

A lokuta da dama, kowace kungiya takan lashe wasa a gidanta, sai dai idan an fi karfinta sosai.

Abin da ya kamata a yi domin magance wannan matsalar shi ne gwamnati ta dauki alkalan wasa na dindindin aiki, ta rika biyansu albashi, sannan ta rika tura su wasannan, sannan yadda alkalin wasa ya yi aikinsa, a rika masa karin girma ko akasin haka. Sannan a tabbatar suna zuwa horo lokaci bayan lokaci.

Rashin masu kula da lafiya

Yadda Chieme ya mutu a makon jiya, ya tabbatar da cewa babu, ko kuma babu kwararrun ma’aikatan lafiya. Yana tsaye, ya yanke jiki ya fada, sannan abokanan wasansa suka ta yin fama da shi wajen taimaka masa ya yi numfashi ta hanyar bude masa baki da danna masa ciki.

Da a ce akwai ma’aikatan lafiya, da sun ba shi taimakon farko, wanda hakan zai taimaka wajen farfado da shi kafin a kai shi asibiti.

Ya kamata a ce kowace kungiya tana da akalla ma’aikatan lafiya guda biyu, da za su rika duba ’yan wasansu kafin a fara wasa.

Sauran matsalolin sun hada da cin hanci da rashawa, ta yadda da dama daga cikin kungiyoyin suke karbar kudaden ’yan wasa domin su sanya su a wasa.

Laifin kocin Super Eagles

A wani laifin dabam da ba kowa yake lura da shi ba, da a ce kocin Super Eagles yana amfani da ’yan wasan da suke buga gasar Firimiyar Najeriya din, da hakan zai sa ’yan wasan su rika dagewa wajen kara kwazo.