✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwan da kan hana ciwo ko cuta warkewa

Ni ina so ne na san abubuwan da kan hana ciwo da cuta warkewa da wuri. Kuma ko shi ake kira kanjiki? Amsa: Abubuwan da…

Ni ina so ne na san abubuwan da kan hana ciwo da cuta warkewa da wuri. Kuma ko shi ake kira kanjiki?

Amsa: Abubuwan da kan taimaka wajen hana ciwo ko cuta saurin warkewa suna da dan dama, kuma sun hada da:

1. Shekaru: Yawan shekaru (tsufa) kan hana ciwo saurin warkewa. Ke nan karancin shekaru kan taimaka wa ciwo saurin warkewa. Wannan a ciwo ke nan kamar gyambo ko targade ko karaya. Amma a cututtuka masu yaduwa kamar wadanda kwayoyin cuta kan kawo su, karancin shekaru da yawan shekaru na iya zama nakasu ga warakar ciwo. Misali ciwon amai da gudawa yanzun nan zai iya kai karamin yaro da tsoho Lahira, amma da wuya ya yi sanadin mai matsakaitan shekaru.

2. karfin garkuwar jiki: Mutane masu lafiyar jiki da garkuwar jiki sun fi saurin yakar ciwo ko cuta a jikinsu fiye da masu raunin garkuwar jiki. Abubuwan da kan sa raunin garkuwar jiki kuwa har da su kansu shekaru, yawa da karancin shekaru na nufin raunin garkuwar jiki, amma matsakaitan shekaru na iya nuni da karfin garkuwar jiki. Amma fa ba a kowane mai matsakaicin shekaru akan samu garkuwar jiki kwakkwara ba, domin masu ciwon suga da kanjamau duk da wasunsu suna da kuruciya, garkuwar jikinsu ba ta da kwari.

3. Abinci: Mutane masu cin abinci hadadde kuma mai lafiya wato (balance diet) a kullum sun fi iya yakar ciwo ko cuta a jikinsu ta yadda ciwo ko cuta za su fi warkewa da sauri saboda abinci mai lafiya shi ne ginshikin gina garkuwar jiki.

4. Yanayi: Yanayin gari, walau na sanyi ko na zafi, ko na ruwa shi ma zai iya shafar saurin warakar ciwo. Shi dai jiki ya fi son yanayi mai dama-dama, dan sanyi kadan ba zafi sosai ba, amma mai danshi. Shi ya sa a misali, za ka ga an fi yi wa yara kaciya lokacin da gari ya yi sanyi saboda ta fi warkewa a irin wannan yanayi.

5. Muhalli: shi kansa muhallin da dan Adam yake zaune a ciki zai iya taimaka masa wajen yakar ciwo ko ya ta’azzara shi. Wato a unguwanni masu kazanta za a iya samun cututtuka iri-iri kuma su ki saurin warkewa akasin a unguwanni masu tsabta, wadanda babu cinkoso ba kura babu kwatami, ba bola ko shara a titi ko’ina.

6. Shaye-shaye: Shan sigari da giya da shaye-shayen miyagun kwayoyi su ma sukan hana cuta saurin warkewa domin suna lalata garkuwar jiki

7. Magunguna: Akwai wadansu da ba shaye-shaye suke yi ba, amma an ba su magunguna masu rage kaifin garkuwar jiki a asibiti. Su ma za su iya saurin daukar cututtuka masu yaduwa kuma su ki warkewa da wuri. Idan aka samu haka akan yi wa mai daukar magungunan kashedi da hanyoyin da zai kare kansa daga cututtuka 

8. Damuwa: Rashin samun isasshen hutu da yawan damuwa su ma suna kassara kwayoyin garkuwar jiki ta yadda jiki ba zai iya yakar ciwo ko cuta cikin sauri ba.

9. kiba: Haka kiba ma take yi wa kwayoyin garkuwar jiki, su yi rauni ta yadda ba za su iya yakar ciwo ba. Shi ya sa masu kiba kusan kullum suna cikin laulayi.

Wai mutum mai shekara 60 zai yi ya zama cikin koshin lafiya?

Daga Ahmad Bichi.

Amsa: Tunda shekaru sun fara ja, za a yi maka fatan kada ka samu hawan jini ko ciwon suga ko na zuciya ko na daji, domin wadannan cututtuka su suke ajalin akasarin mutane masu yawan shekaru a irin kasashenmu. Shekarun kasa da haka kuma an fi ganin haddurran ababen hawa suna sanadin rayukan samari. 

To me za ka yi kenan ka ga ka guji wadancan cututtuka? A hakikanin gaskiya wannan ya danganta da tarihin lafiyar iyayenka ko wani dan uwa na jini, domin idan a iyaye ko yayye akwai wanda ya yi fama da daya daga cikin wadancan cututtuka da aka lissafa a sama to sai dai addu’a. Duk da haka dai za ka iya guje wa wasu cututtukan idan kana guje wa duk abubuwan da aka lissafa a tambayar farko masu kawo ko hana cututtuka waraka. Wato ka guji kiba, ta hanyar yawan motsa jiki, amma ka ci mai kyau ka sha mai kyau, wato ka ci lafiyayye kuma hadadden abinci mai dukan sinadarai na sa kuzari da gina jiki da masu bitamin da sauransu a kullum. Misalin hadadden abinci shi ne tuwon masara miyar kuka da man shanu da tsokokin nama da lemon fata idan ka kai. Ko shinkafa da salad da kifi da gwanda a gefe. Ka guji shaye-shaye, wato giya da sigari da kwayoyin da ba likita ya rubuta maka ba. Ka guji damuwa, wato ka rika samun yawan hutu da barci da nishadi. Ka guji kazamin wuri, wato ka zama cikin tsabta da muhalli tsabtatacce. Sa’annan daga karshe ka guji yanayin da jikinka ba ya so, wato ka guji shiga rana.

Da gaske ne kwanciya a cikin hasken fitila yana iya hana samun wadataccen barci?

Daga Mukhtar Gafai, Katsina

Amsa: Eh, da gaske ne. Ka san akwai agogon jiki da muka sha bayani a kai a nan, wato circadian rhythm. Shi wannan agogo yana aiki da lokaci da haske da sauran yanayi. Fitowar rana da fitila mai haske suna iya rikita agogon ya dauka cewa ba lokacin barci ba ne, ya rika yi maka kara a kwakwalwa ka tashi. Shi ya sa ake so a rika kashe fitilu domin wannan agogo ya bar ka ka natsu ka yi barci yadda ya kamata. Bincike ne ya tabbatar da haka. Kuma a kasashen da suke da rana awa 24 lokutan zafi da dare awa 24 lokutan sanyi sukan yi korafin rashin samun isasshen barci watannin da rana kan ki faduwa.

Me ke sa wadansu ke yin tauna ko surutu a cikin barci?

Daga Nasiru Kainuwa, Hadeja

Amsa: Wannan ba ciwo ba ne. Da magagi, da sambatu da tauna a cikin barci duk ba ciwo ba ne, bambancin halitta ne, saboda wani barcinsa ya fi na wani nauyi.