✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa hudu da bai kamata ka karya su ba a rayuwa

Ya ku mabiya da makaranta wannan muhimmin shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum! Bayan haka, ina yi muku…

Amana tamkar kwai ce, tana bukatar kulawa ta musamman!Ya ku mabiya da makaranta wannan muhimmin shafi na Sinadarin Rayuwa, ina yi muku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum! Bayan haka, ina yi muku Barka da Sallah, Allah Ya maimaita mana ta badin-badada, amin.
Ina yi muku barka da sake saduwa, bayan dogon nukusanin da filin ya yi na kimanin makonni biyar, wanda haka ya faru ne a sakamakon hutun shekara da na dauka. Yanzu kam na dawo, kuma da yardar Allah za mu ci gaba da zizara wa junanmu sinadaran da za su ci gaba da sassaita mana rayuwa. Allah Ya sa mu dace, amin.
Kamar yadda kanun bayani ya gabata a sama, a wannan karon, za mu tattauna ne game da wasu tubalan rayuwa guda hudu, wadanda suke da tsananin muhimmanci. A duk lokacin da mutum ya dube su, zai ga cewa su ne sinadaran da kan karfafa rayuwa, suke karfafa danganta tsakanin al’umma, sannan kuma su samar da kwanciyar hankali da ci gaba a rayuwar al’umma gaba daya.
Wadannan karfafan tubalan rayuwa guda hudu da za mu duba a yau su ne: Na daya – Amana. Na biyu – Alkawari. Na uku – Zumunci. Na hudu – Zuciya/Soyayya. Kamar yadda na ambata a baya, wadannan tubala, suna da tsananain muhimmanci a rayuwa. Kuma abin da ya sa ya zama abu mai kyau cewa kada ka sake a rayuwarka ka karya daya daga cikinsu shi ne, saboda a duk lokacin da ka karya su, to ba fa za su yi kara ba, ba za su yi taratsi ba, amma dai kunar ciwonsu yana da tsanani kuma zai iya haifar da kowace irin tsintsinar tsiya ga rayuwar wanda ka karya mawa, sannan kuma sakamakon ya shafi al’umma gaba daya.
Amana: Amana wata babbar jigo ce da ke sanya dan Adam ya zama kammalalle, wadda ke daukaka duk mutumin da ya rike ta, sannaan ga duk al’ummar da ke rike amana, za ta kasance bunkasassa kuma ingantattar al’umma. Al’umma mai ci gaba, mai cin nasara ga dukkan yanayi.
A lokacin da mutum aka ba shi amana, to lallai ne ya yi iyaka kokarinsa ya rike ta yadda ya kamata, ya hannanta ta ga wanda ya ba shi idan lokacin ya yi. Idan kuwa Shiadan ya fitsare wa mutum zuciya, aka ba shi amana ya kasa rikewa, ya ci; to babu shakka zai kasance wulakantacce. Maci amana yakan zama marar kima ga mutumin da ya ci wa amana, yana zama wulakantacce, marar mutuminci ga al’ummar da yake rayuwa a cikinsu.
Bari in ba ku wani misali, kila mu fahimci darasin ta haka. dauki misalin a ce kai ne kake zaune a Kaduna, iyalinka suna Kano. Aka bugo maka waya cewa ga matarka ba ta da lafiya, kai kuma kana cikin wani uzurin da zai hana ka iya zuwa Kano da gaugawa. Matarka ta je asibiti, aka rubuta mata magani, kai kuma sai ka samu wani abokinka da zai je Kano a lokacin, ka ba shi amana, ka ba shi Naira dubu ashirin don ya kai wa matarka ta sayi magani. Abokin nan naka ya isa Kano, amma ya ci amana, ya ki kai kudin nan. Sanadiyyar haka, matarka ta rasa maganin da likita ya rubuta mata, ciwo ya ta’azzara, karar kwana ta zo, ta mutu. Shin da wane ido za ka rika kallon abokin nan naka? Kuma a ganinka, idan sauran al’umma suka samu labarin abin da ya aikata na cin amana, da wane ido za su kalle shi?
Na tabbata a wannan karon ba sai na kara bayani ba, hoton ma’anar darasin nan ta fito karara. Domin kuwa kowa zai ga irin ta’asar da mutumin ya aikata. Na farko dai ya haddasa ko ya taimaka wajen rasa rai. Matar nan da ta mutu, kila tana da ’ya’yan da ke bukatar kulawarta, tana da mijin da ke bukatar tallafinta. Amma saboda cin amana, an yi sanadiyyar salwantar rayuwarta.
A gefe daya kuma, za mu iya ganin yadda mutumin nan ya barranta kansa daga dukkan wata hanya ta kirki, domin kuwa tun daga lokacin da ya aikata wannan cin amana, ke nan ya raba zumunci da amincin da ke tsakaninsa da abokinsa da ya ba shi amana. Haka kuma ya yi wa kansa bakin tambari, wanda ba zai taba goguwa ba daga faifan tarihin rayuwarsa. Idan ba a yi sa’a ba ma, bakin tabon bakin halin nasa zai yi yado ya bibiyi har ’ya’yansa da jikokinsa.
Wannan ke nuna mana muni da illar cin amana. Dalili ke nan ya sanya a wannan fili muke karfafa tambihin cewa, mu daure, mu jure wa zukatanmu, mu yaki Shaidan, mu kaurace wa cin amana. Abin da a kullum za mu sanya a zuciya shi ne, shin za mu so wani ya ci amanarmu? Amsa – a’a. Idan haka ne kuwa, to kada mu sake mu aikata wa wani abin da muka san ba mu so a aikata a kanmu.
Allah Ya kiyaye, ya yi mana jagora a rayuwa amin. A mako na gaba, za mu ci gaba da wannan maudu’in insha Allah!