✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa hudu da bai kamata ka karya su ba a rayuwa (4)

Ya ku ma’abuta bibiyar filin nan na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku sallama kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum. Bayan haka, kafin in karkare maudu’inmu…

Soyayya rayuwa ce, kada a karya ta!Ya ku ma’abuta bibiyar filin nan na Sinadarin Rayuwa, ina yi maku sallama kamar yadda muka saba, Assalamu alaikum. Bayan haka, kafin in karkare maudu’inmu da muka faro makonni uku da suka gabata, zan yi kokarin bayyana sakon wata baiwar Allah, wacce ta aiko mani da shi a farkon makon nan, bayan ta karanta kashi na uku na maudu’in namu. Zan sakaya sunanta da lambarta, saboda kariya. Ga abin da ta ce:
“Assalamu alaikum. Zumunci a yanzu ba kowa ya san muhimmancinsa ba. Ni kam na tsani ’yan uwana, ba na kaunarsu kwata-kwata saboda sun raba ni da gidanmu, bayan rasuwar mahaifana duka biyu. A matsayina na mace, wallahi ba na son ganinsu, ko jin labarinsu. Sun bi ni da sharrin da ba zan taba manta su a rayuwata ba. Idan da ana canza dangi, da na canza su.”
To, fa! Malama, al’amarin nan kuwa ba ya da dadin ji amma duk da haka ya kamata ki sake natsuwa, ki yafe masu, domin kuwa kila jarabawa ce Allah Yake maki da wadannan karkatattun dangi. Idan kika biye ta tasu, za ki shiga cikin fushin Allah. Babu dacewa ko kadan, mutum ya ce zai rama mugunta da mugiunta. Abu ne mai kyau, ka kyautata wa wanda ya munana maka. Idan ka yi haka, ka yi maganinsa, domin kuwa za ka samu farin ciki mai yawa, sannan kuma ka samu sakamako mai girma daga wurin Allah. Don haka, ina ba ki shawara, ki tausashi zuciyarki, ki yafe masu. Ki samu hanyar da za ki maido da alakar zumunci a tsakaninku, domin kuwa a rayuwa, wajibi ne ka yi tarayya da dan uwanka na jini. Ki karanta tarihin Manzon Allah (SAW), yadda ya sha daga da ’yan uwansa na jini amma sannu a hankali ya mayar da komai ba komai ba, ya sasanta da su, duk da irin cin kashin da suka yi masa. Daga bisani kuma ya samu nasara a kansu, masu rabo suka tuba, suka amshi shiriya, tababbu kuwa suka halaka. Allah Ya sa mu fi karfin zukatanmu, Ya ba mu karfin halin yafe wa wadanda suka zalunce mu, Ya kuma ba mu karfin gwiwar kyautata wa wadanda suka kware mu. Amin. – Sinadarin Rayuwa.
A yanzu kuma zan karkata zuwa ga ci gaba da maudu’inmu  da muka faro, mai taken ‘Abubuwa hudu da bai kamata mu karya su ba a rayuwa.’ A makonni uku da suka gabata, mun yi bayani game da tubala uku, wato ‘Amana’ da ‘Alkawari’ da ‘Zumunci.’ Don haka a yau kuma za mu yi tambihi ne a kan cikon daya tubalin na hudu, wanda bai kamata mu karya ba a rayuwa. Wannan kuwa tubali shi ne ‘Zuciya’ ko kuma mu kira shi da ‘Soyayya.’
Tun farko dai ita kauna ko soyayya a zuciya ake ajiye ta. Kuma da zarar an dauki kauna ko so aka saka a zuciya, to sukan babbake ko’ina cikin zuciyar. A lokacin da namiji ya dauki kaunar wata ya saka a zuciyarsa ko kuma wata ta dauki kaunar wani ta saka a zuciyarta, shi ke nan, aikin gama ya gama. A duk abin da mutum zai yi sai ya tuno da wannan mace ko kuma sai ta tuno da shi. A lokacin nan zuciya za ta kasance cikin rashin sukuni, idan aka samu wani akasi. Wannan yana nuna mana irin tasiri da muhimmancin da ke tare da kauna ko soyayya kuma hakan ke nuna mana cewa lallai ne mu yi taka-tsan-tsan da kula da amanar kauna tsakanin juna.
Wani gargadi na musamman da ya kamata mu yi wa juna game da wannan tubali shi ne, cikin tubalan nan hudu, karya zuciya ko soyayya ya fi hadari, domin yana iya jawo mutuwa ga mutum. Za ka iya cin amanar mutum ya daure ya ci gaba da rayuwarsa. Za ka iya karya alkawari, radadin haka ya gallabar da mutumin da ka yi wa haka amma bayan wani lokaci yana iya mancewa ya ci gaba da harkokinsa. Za ka iya raba zumunta amma abin ya wuce, amma a lokacin da ka karya wa mutum zuciya, ka jefar da kaunar da ke tsakaninku, babu shakka zuciyar na iya bugawa, musamman saboda kimar da ke ga zuciyar a jikin dan Adam.
Don haka, tun farko idan ka san cewa ba tsakani da Allah kake son mace ba, kada ka sake ka bari ta sanya kaunarka a zuciyarta. Haka ke ma, kada ki sake ki bari wani masoyinki ya saka ki a zuciya, idan kin san cewa ba kaunar gaskiya kike masa ba. Illar haka shi ne, ranar da karshen al’amarin zai zo, idan ka ce za ka karya mata zuciya, to komai yana iya faruwa. Allah Ya kiyaye! Don haka, mu kiyayi karya zuciya, mu tsaya mu yi kauna ko soyayya ta gaskiya. Allah Ya sa mu dace, amin!