✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa hudu da bai kamata ka karya su ba a rayuwa (2)

Ya masu bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Ina kara taya mu murnar Babbar Sallah. Allah Ya maimaita mana, mu ga ta badin-badada lafiya. Bayan…

Ya masu bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, assalamu alaikum. Ina kara taya mu murnar Babbar Sallah. Allah Ya maimaita mana, mu ga ta badin-badada lafiya. Bayan haka, a wannan makon za mu ci gaba da kashi na biyu na maudu’in da muka faro a makon jiya, mai take na sama.
A makon na jiya, mun warware tubali na farko kuma muka gabatar da takaitaccen bayani game da shi. Mun yi bayani ne game da ‘Amana,’ inda a wannan makon kuma za mu warware tubali na biyu, wato ‘Alkawari.’
Alkawari: Masu azancin magana sun ce alkawari kaya ne. Don haka, alkawari wani babban al’amari ne mai matukar muhimmanci a rayuwar al’umma. Kasancewar shi tamkar kaya, to kuwa wajibi ne ga mutumin da ya nada gammo ya dauke shi, to kuwa ya ajiye shi daidai inda ya dace. Kada mutum ya ce zai dauki alkawari sannan kuma ya ce zai karya.
Kamar yadda amana take da tasiri da muhimmanci wajen bunkasa al’umma, haka shi ma alkawari yake, domin kuwa tamkar ta masu salon magana, danjuma ne da danjummai. A duk lokacin da mutum ya dauki wani muhimmin alkawari, sannan kuma ya cika shi a daidai lokacin da ya dauka, to kuwa babu shakka za ka ga ya samu shaida daga al’umma. Cika alkawari na sa mutum ya zama mai gaskiya kuma abin gaskatawa. Haka kuma, mutum zai kasance mai daraja da muhibba, a lokacin da ya zama mai cika alkawari. A yayin da kuma mutum ya zama marar alkawari, to zai zama marar mutumci, zai zama mutumin banza a cikin al’ummarsa.
Mutum marar cika alkawari, yakan zama abin kyama kuma abin gudu ga mutanen kwarai. Idan shi dan kasuwa ne, abokan hulda ba za su rika amince masa ba. Idan kuwa mutum ya rasa abokan hulda a kasuwanci, babu abin da zai biyo bayan mu’amalarsa sai asara da rashin nasara.
Bari mu doka misali da kawunanmu, domin dai mu samu darasin maudu’in nan sosai. Ya kai mai karatu, dauki misalin kai manomi ne, ka noma hatsinka mai yawa. Rannan sai wani dan kasuwa ya yi maka alkawarin zai saye shi gaba daya. Kun gama kulla ciniki, ya ce maka ka dauki hayar tirela guda, ka kai masa hatsin nan garinsu. Ya ce maka da zarar ka isa garin nasu da hatsin, zai biya ka kudin hatsin da kuma kudin motar dakon kayan. Ba ku yi awa daya da kulla ciniki ba sai ga wani dan kasuwar da motarsa, ya nemi ka sayar masa da hatsin nan. Kai kuma saboda alkawari, sai ka ki sayar masa, ka gaya masa cewa ka riga ka sayar da shi.
Wanshekare, ka dauki hatsin nan ka nufi garinsu amma da ka isa sai ya fara yi maka kame-kame. Daga karshe dai ya karya alkawari, ya ce maka ba zai saya ba. To don Allah yaya za ka ji a ranka? Ba kai kadai ba, yaya masu motar da ka dauko za su ji? Shin idan ka ba da labarin abin nan da ya faru ga mutane, yaya za su dauki wannan dan kasuwa? Kuma kai karan kanka, kana jin za ka iya ci gaba da mu’amalar kasuwanci da shi a nan gaba?
Babu shakka, a sanadiyyar wanan karya alkawari, mutumin nan zai zama marar mutunci a idanun jama’a. A sanadiyyar wannan aika-aika da ya yi, ya bata wa mutane da yawa lokaci, ya jaza wa manomin nan asara, sannan kuma ya sanya shi cikin kunci. Don haka lallai karya alkawari babban sharri ne da ba ya haifar wa kowa da mai ido.
Irin wannan illar ce ta sanya ake gargadin jama’a da cewa lallai mu guji karya alkawari. Tun farko idan mutum ya san cewa abu ya fi karfinsa, to kada ma ya ce zai dauki alkawari; domin kuwa yana da sanin cewa ba zai iya cika shi ba. Kuma har kullum ya kamata mu gane cewa, duk wani abu mai muni da muka san cewa ba mu so a aikata mana, to kada mu sake mu mu aikata wa wasu.
Cika alkawari dai abu ne mai kyau kuma abin kirki ga al’umma. Babu wani addini na duniya da ba ya kishin mai cika alkawari. Haka kuma kowane addini yana kira ga mutane da su zama masu cika alkawari. Don haka mu kasance masu cika alkawari, domin mu taimaki kanmu kuma mu taimaki al’umma.
Idan Allah Ya kai mu makon gobe, za mu ci gaba da warware jigon nan, inda za mu shiga tubali na uku daga cikin tubala hudu na abubuwan da bai kamata mu karya su ba a rayuwa.
Za mu ci gaba