✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 5 da ke samar da mai (2)

Idan za a iya tunawa, mun ce dutsen mafari (source rock) na dauke da kofofi (Pores), to ta cikin wadannan kofofin ne sinadaran ‘hydrocarbons’ wadanda…

Idan za a iya tunawa, mun ce dutsen mafari (source rock) na dauke da kofofi (Pores), to ta cikin wadannan kofofin ne sinadaran ‘hydrocarbons’ wadanda suka narke suke yin kaura zuwa ko dutsen mafari ko kuma dutsen tafkin mai. Yawan samuwar kofofi ake kira ‘High Porosity’ (hai forositi) hakan kan kawo mai mai yawa ya yi kaura cikin kankanen lokaci.  
Baker (1980), wani masani kan mai, ya ce ruwa na taimakawa wurin samar da kaurar mai, kasancewar a kowane lokaci idan aka hada ruwa da mai; mai na kasancewa a saman ruwa, kuma idan ruwa ya rika motsawa, mai ma zai rika motsawa.
Ya bayar da hujjar cewa kowa yana da tabbacin akwai ruwa a cikin kasa, wanda ake kira ‘underground water’, wanda kuma shi ya sa ake samun ruwa idan an tona rijiya. To ruwan da yake cikin kasa ne, a lokacin da yake motsawa, sai ya rika motsa mai, har ya sanya ya yi kaura.
Wasu masana sun ce ruwa ba ya taka rawa wurin samar da kaurar mai. Suka ce a lokacin da zafi ya narkar da sinadaran ‘hydrocarbons’, akwai sinadaran da suke fara narkewa inda kuma kasancewar sinadarin ‘kerogen’ ne ke samar da mai, to sai wadannan sinadaran da suka narke su rika tafiya da sinadarin ‘kerogen’. Wadannan sinadarai kuwa kan yi kaura ta kofofin da ke jikin dutsen mafari. Cikin masanan da suke yarda da hakan akwai Tissot da Welte, 1978 da Hunt, 1979 da kuma McAuliffe 1979.
Wadansu masana kuma sun ce idan zafi ya turara sinadaran ‘hydrocarbons’, sai su fara karo da juna, hakan ne kuma zai sanya su rika yin kaura ta kofofin da ke jikin dutsen mafari. Masana da dama sun amince da wannan hanyar, sai dai Dickey 1975 da Magara 1980 ba su yarda da wannan hanyar ba.
Amma dai ko ma wace hanya ce, dukan masanan sun yarda idan har babu kaura, to kuwa ba za iya hakar mai ba, sun kuma yarda zafin ne yake sanya mai ya yi kaura.

(5) Tarko
Jama’a da dama kan yi mamaki, shin me ya sa ba a samun man fetur a kowane wuri? Baya ga haka kuma, tun da mai kamar ruwa ne, me ya sa ba ya tafiya daga wannan gari zuwa wancan? Ko kuma me ya sa ya tsaya a wurin daya kawai?
Amsar dukkan wadannan tambayoyi ta ta’allaka a kan abu daya, wato samuwar tarko. Tarko ne ke taimakawa wurin taskance mai a wuri daya, ba tare da ya motsa zuwa wani wuri ba. Akan samun tarko ne ta hanyar girgizar kasa da ‘tsunami’.
An samu tarko lokacin samuwar duwatsu da ake kira ‘orogeny’; sannan an samu tarko lokacin da aka samar da duniya, kamar yadda masana suka ce. Su wadannan tarko su ake kira ‘faults’ da ‘folds’ da kuma dutsen ‘cap rock’ (kaf rok).
Sakamakon abubuwan da na lissafo a sama, sai a samu mafarin dutse ko tabkin dutse ya lankwashe wato ya rika hawa da sauka har ya bayar da surar ‘folds’, ko ya karye ko kuma ya rubza. Karyewar ko rubzawar dutse ko shimfidar dutse ake kira ‘faults’, lankwashewar dutse kuma ake kira ‘folds’. Wani lokaci akan samu tarko idan dutsen ‘cap rock’ ya kasance a saman shimfidar ko dutsen tafki. Dutsen ‘cap rock’ kan hana fitar mai bayan ya shiga shimfidar ko dutsen tafkin mai. Wannan dutse baki ne, suwal-wal kuma ba shi da kofofi a jikinsa.
Samuwar mai
A nan zan yi bayanin yadda wadannan abubuwa biyar da na lissafa suke haduwa su samar da mai. A lokacin da dutsen mafari ke shigewa cikin kasa sakamakon samuwar sabbabin kwayoyin duwatsu (sediments) a samansu, yanayi kan canza, wanda a lokacin da suke waje akwai iska, amma a lokacin da suke kara shiga ciki babu iska. Sannan yanayin yakan kara zafi. Wannan zafin da kuma rashin iska sai ya sanya sinadarin ‘kerogen’ da ke cikin dutsen mafari ya fara dagwargwajewa. Wannan dagwargwajewar ake kira ‘cracking’ (kirakin).  
Masu magana sukan ce, ‘idan gyada ta sha matsa, sai ta yi mai, don haka a lokacin da aka kara samun wadansu duwatsu a saman dutsen mafari (source rock) sai nauyi ya sanya sinadarin ‘kerogin’ ya fara fitar da mai, musamman ma idan akwai isasshen zafi.
Wani abu da nake so mai karatu ya fahimta shi ne, akwai kofofi a jikin dutsen mafari, inda kuma sai mai ya rika naso walau zuwa wani dutsen mafari ko kuma dutsen tafki. Wannan nason da yake yi shi ake kira kaura (migration). Bayan ya yi kaura ne sai ya shiga dutsen tabki, wanda kuma da ma yana dauke da tarko, wannan tarkon ne zai taskance man. Daga nan sai a gudanar da bincike, bayan an tabbatar da samuwar mai sai a hako shi.
A shekarun baya, an yi ta samun jan-kafa wurin aikin hakar mai da ke yankin Tafkin Chadi, inda wadansu suka yi hasashen babu mai a yankin. Hakan ya sanya zan yi bayani kan samuwar mai ko akasin hakan a yanki Tafkin Chadi (Chad Basin) da ke Jihar Barno, zan yi bayanin ne bisa ga abubuwa biyar da na lissafo a sama.
Dutsen mafari
Tafkin Chadi na kunshe da dutsen mafari da ake Gongila ko Fika Shale. Shimfida ko dutsen Gongila na dauke da sinadarin ‘hydrocarbons’ kashi 1.5 a cikinsa, inda kuma  dutsen ko shimfidar Fika Shale ke dauke da sinadaran ‘hydrocarbons’ da ya kai kashi 0.9 a cikinsa.  Masana sun ce idan har shimfida ko dutse mafari ya samu kashi 0.5 na sanadarin ‘hydrocarbon’, to zai iya zama dutsen mafari.
Dutsen Tafki
A bisa ga bayanin da masana suka yi, sun bayyana dutse ko shimfidar dutsen Gombe Sandstone da Keri-Keri na da inganci ko nagartar da za su zama dutsen tafki.  Wadannan shimfidun duwatsu suna dauke da kofofi da kuma tarko da za su iya taskance mai.
Zafi
Sakamakon bincike da aka gudanar, an gano dutsen mafari yana da nisan mita 300 a karkashin kasa, sannan akwai zafin da ya kama daga 60 zuwa 120 a ma’aunin digiri sentigired (Degree Centigrade). Idan ba a manta ba na ce zafi daga 60 zuwa 150 ne ke iya sanya sinadaran ‘hydrocarbons’ su fara narkewa. Idan kuwa haka ne tafkin Chadi ya cika sharadin zafin da zai iya narkar da wadannan sinadarai.
kaura
Bincike ya bayyana akwai kofofi (pore spaces) a jikin dutsen mafari na Fika Shale, don haka bisa ga tabbatacin akwai isasshen zafin da zai iya narkar da sinadaran ‘hydrocarbon’, to kuwa akwai kofofin da wadannan sinadarai za su iya kaura. Baya ga haka, a jikin dutsen tafkin mai, Gombe Sandstone da kuma Kerri-Kerri akwai hanyoyin da man zai iya shiga.
Tarko
Alkaluman bayanai kan samuwar duniya sun bayyana an samu tarko a Tafkin Chadi cikin shekarar Jurassic da kuma Santonian. Santonian da Jurassic wadansu shekaru ne da suka taka rawa wurin samuwar nahiyoyin duniya. Wadannan shekaru suna cike da ayyukan samuwar duwatsu da zaizaiya da lankwashewa da kuma karyewar shimfidar duwatsu. Wadannan ayyukan ake kira ‘tectonic actikities’ (tektonik aktibitis). Wadannan ayyukan ne suka samar da tarko a tafkin Chadi.
Wannan ita ta kawo karshen takaddamar walau akwai mai a Tafkin Chadi ko babu.
Ina ba mai karatu tabbacin akwai mai a Tafkin Chadi, sai dai kawai a hako shi.

Za a iya samun Bashir Musa Liman a [email protected]; ko [email protected]; ko [email protected]; 07036925654