✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 5 da ke hana waya saurin caji a lokacin zafi

Da yawan wayoyin hannu suna fama da wasu abubuwa da ke kawo musu tarnaki wajen yin caji.

Yawancin mutanen da ke amfani da wayoyin hannu na korafi kan rashin saurin caji, sai dai sun gaza gano a ina gizo ke sakar.

Da yawan wayoyin hannu suna fama da wasu abubuwa da ke kawo musu tarnaki wajen yin caji, wanda hakan yake sa wa su dauki tsawon sa’o’i suna caji.

Ga dalilai biyar da ke hana waya saurin caji:

1. Amfani da waya lokacin da ta ke caji:

Mutane da yawa ba su san cewar amfani da waya a lokacin da ta ke caji na hana yin caji cikin sauri ba. Dalili kuwa shi ne waya ta kan dauki zafi lokacin da ta ke caji, sannan wasu manhajoji kan zuki caji a lokacin da ake amfani da ita.

2. Akwai manhajojin da ke saurin zuke caji:

Yana da kyau mai amfani da waya ya binciki wayarsa don sanin manhajojin da ke da saurin zuke cajin waya. Wadannan manhajoji kan hana waya saurin daukar caji sakamakon yadda suke yi mata sukuwar sallah.

3. Igiyar wayar caji:

A lokuta da dama igiyar wayar caji kan iya zama sila na rashin saurin cajin waya. Wani kuma ya kan iya kasancewa wajen da ake saka cajin wayar ne ya samu matsala.

4. Abun caji mara kyau ko nagarta:

A wani lokacin ma abun cajin (charger) ne zai iya kasancewa mara kyau ko nagarta. A lokuta da yawa hakan na iya sa waya ta dauki tsawon lokaci tana caji amma ba ta samu cajin kirki ba.

5. Wuta mara karfi:

A wasu lokutan rashin wuta mai karfi kan haifar da rashin saurin cajin waya. Kowane abun cajin waya yana da adadin wutar da yake so domin bai wa waya damar yin caji yadda ya kamata.

Yana da kyau masu amfani da wayoyi su san ire-iren matsalolin da ke tattare da wayoyinsu don sanin yadda za su shawo kan su.